Header Ads

Hukumar Kwastan ta yi magana kan harbin da aka yi a wani shingen ta da ke jihar Jigawa

Shugaban hukumar kwastan ta Nijeriya, Hameed Ali

Hukumar Kwastan ta Nijeriya ta bayyana cewa ba ta ji dadin harbin wani jami'in kwastan wanda ya ki tsayawa a mota a wani shinge da wani dan uwansa jami'i ya yi ba.

Jami'in, Muhammad Sayyadi, a ranar Juma'a yana dawowa ne daga Jamhuriyar Nijer, kuma ya ki tsayawa a wani shinge a Kargo da ke karamar hukumar Garki domin yin bincike inda hakan ne ya tilastawa jami'an bude wuta a matarsa.

Sai dai cikin rashin sani, Malam Sayyadi, jami'i ne da ke aiki a shiyyar hukumar Kwastan ta jihar Legas ke tuka motar.

Malam Sayyadi danda ne na Sarkin Ringim, Sayyadi Mahmoud. Ringim na daya daga cikin manyan masarautun jihar Jigawa guda biyar.

Kakakin hukumar kwastan a shiyyar Jigawa/Kano, Nura Saidu, ya bayyana cewa hukumar na gudanar da bincike cikin al'amarin.

"Muna nuna matukar tausayawarmu ga duka wadanda wannan mummunan al'amari ya samu, kuma muna tare da iyali da abokai na wanda wannan abu ya shafa.

"A matsayinta na hukuma, muna tabbatar maku da cewa hukuma za ta yi cikakken bincike cikin al'amarin domin gano me ya haifar da shi da duk wasu abubuwa dangane da shi.

"Abinda muka fi bukata shine kasancewa cikin lafiya da tsaron wanda abin ya shafa da sauran al'umma a wannan lokaci na jarabawa.

"Muna so mu tunatar da ku cewa hukumar ta sa muhimmanci sosai wajen ruke bindigogi yadda ya kamata. Harbe-harbe bisa kuskure abubuwa ne da za a iya hana afkuwarsu, domin duka jami'ai an koyar da su a tsanake yadda za su kare tare da amfani da bindigogin su a inda ya dace a kuma muhallin da ake sawa ido.

"Za mu cigaba da samar da bayanai a yayin da binciken ke cigaba da faruwa tare da kuma bayan an samu bayanai masu yawa." Kamar yadda Malam Sa'idu ya bayyana.

No comments

Powered by Blogger.