Koriya ta Kudu ta yi murnar harba rokar da ƙasar ce ta ƙera shi cikin nasara
Yayin da aka harba rokar Nuri wadda kasar Koriya ta Kudu ta kera daga tashar Naro Space Center a ranar 25 ga watan Mayu na shekarar 2023 - AFP
Kasar Koriya ta Kudu a ranar Alhamis ta bayyana cewa ta harba rokar da ta kera mai suna Nuri tare da sa tauraron dan Adam sararin samaniya, inda ta yi murna da babban matakin cigaba da kasar ta samu a shirin ta na sararin samaniya. Harba Nuri din na uku da aka yi shine ya sa tauraron dan Adam na gwaji cikin nasara a sararin samaniya a shekarar da ta gabata bayan rashin nasarar da aka yi a shekarar 2021 bayan yunkurin yin hakan inda mataki na uku na injin din rokar ya kone nan-da-nan.
Rokar wadda ke da matakai uku, da tsawo sama da mita 47 da nauyin tan 200, ya keta sararin samaniya ne da karfe 6:24 na yamma (0924GMT) daga Naro Space Center da ke gabar kudancin kasar Koriya ta Kudun, inda aka ga hayaki mai yawa fari, "Muna sanar da 'yan kasa cewa an harba Nuri karo na uku, wanda aka kirkira domin samar da cigaba ga tafiya sararin samaniyar kasar nan, an harba shi cikin nasara." Kamar yadda ministan kimiyya da fasahar kasar, Lee Jong-ho, ya bayyana.
Akwai sadarwa a tsakanin babban tauraron dan Adam da tashar sararin samaniyar Koriya ta Kudu ta King Sejong Station da ke Antarctica, kamar yadda ya bayyana, inda ya ce harbawar "na yin nuni da karfin mu na harba tauraron dan Adam daban-daban sararin samaniya da kuma binciken sararin samaniya." Kasar Koriya ta Kudu za ta kara harba wasu Nuri din uku zuwa shekarar 2027, kamar yadda Lee ya bayyana.
Shugaban kasar Koriya ta Kudu, Yoon Suk Yoel, ya bayyana farin cikinsa da harbawar da aka yi, inda ya ce hakan zai ba kasar wata dama a cikin kasashen duniya.
"Harba Nuri na uku babban cigaba ne da ke nuna cewa kasar Koriya ta Kudu ta shiga cikin kungiyar G7 masu karfin sararin samaniya." Ya bayyana a cikin wani jawabi. Harbawar da aka yi na zuwa ne kwana daya bayan an dage harbawar sakamakon matsalar da aka samu wajen sadarwa ta na'ura mai kwakwalwa inda aka gyara hakan a ranar Alhamis.
Kasar Koriya ta Kudu na da gurace-gurace dangane da sararin samaniya, ciki har da sauka kan wata zuwa shekarar 2032 da kuma Mars zuwa shekarar 2045.
A nahiyar Asiya, Japan, Sin da Indiya duk suna da shirin sararin samaniya wanda ya cigaba sosai, kuma kasar Koriya ta Arewa wadda ke da Nukiliya ita ce ta bayan nan wadda ta shiga cikin kungiyar kasashen da ke da karfin harba tauraron dan Adam din su. Manyan mizayel da rokokin samaniya suna da fasaha ne iri daya, kuma Pyongyang ta yi ikirarin cewa ta sa tauraron dan Adam mai nauyin kilo 300 a sararin samaniya, wani abinda Washington ta yi Allah wadai da shi cewa gwajin mizayel ne a boye.
Shirin sararin samaniya na kasar Koriya ta Kudu na da tarihi - a harbawa na farko da suka yi sau biyu a shekarun 2009 da 2010, wanda wani bangare ne na fasahar Rasha, duka ba su yi nasara ba. Na farko ya tarwatse bayan minti biyu da tashinsa, inda Seoul da Moscow suka dorawa junansu laifi.
Bayan nan, wanda aka harba a 2013 ya yi nasara, amma ya dogara ne da injin din da kasar Rasha ta samar a matakinsa na farko. A watan Yunin da ya gabata, Koriya ta Kudu ta kasance kasa ta bakwai da suka iya harba tan daya na abu mai fashewa na yaki a rokar su. Mataki na uku na Nuri wani abu ne da aka dade ana yi wanda ya ci kudi won tiriliyan biyu (dalar Amurka biliyan 1.5) kamar yadda kafar watsa labaru ta AFP ta bayyana.
Post a Comment