An bayyana wani Ba'amurka a matsayin mara laifi bayan ya kwashe shekaru 33 a kurkukun California
An bayyana wani dan kasar Amurka a matsayin mara laifi tare da kuma sakin sa bayan ya kwashe shekaru 33 a wata kurkuku da ke Amurka kan laifin yunkurin yin kisan kai.
A ranar Alhamis ne dai lauyan yankin Los Angeles County ya bayyana cewa Daniel Saldana, wanda a yanzu shekarunsa 55, an saki shi bayan cewa shi mai laifi a shekarar 1990 kan bude wuta ga wata mota da ke barin filin wasan kwallon kafa a Baldwin Park da ke gabashin Los Angeles.
Harbe-harben dai ya yi sanadiyyar raunata biyu daga cikin shida na matasan da ke ciki amma sun tsira.
Saldana na daya daga cikin mutane uku da ake zargi da kai harin inda kuma aka yanke masa zaman kurkuku na shekaru 45 bayan an zarge shi da aikata laifuffuka shida na yunkurin yin kisa da kuma zargi daya na harbin motar da ke dauke da mutane.
To sai dai shaidar da aka samu daga daya daga cikin wadanda ake zargi da harin ta fito cewa, "Ba shi cikin harbe-harben ta kowacce fuska kuma baya wurin yayin da al'amarin ya afku."
Mutumin dan shekaru 55 da haihuwa, wanda aka gani tare da Lauyan yankin, George Gascon, ya bayyana cewa ya yi farin ciki da aka sake shi.
"Jajircewa ce, kullum ka farka ka san cewa ba ka da laifi amma ga ka a kulle a kurkuku, kana kuka domin neman taimako." Saldana ya bayyana, inda ya kara da cewa, "Ina cikin farin ciki cewa wannan ranar ta zo."
Lauyan yankin bai yi cikakken bayanin shari'ar Saldana ba, amma ya nemi gafarar iyalansa, inda ya ce, "Na san wannan ba zai dawo da kai baya ba shekarun da ka yi a kurkuku, amma ina fatar neman gafarar mu za ta kawo kwanciyar hankali kadan gare ka a yayin da za ka fara sabuwar rayuwarka."
"Wannan ba wai kawai bala'i ba ne na saka mutane cikin kurkuku kan laifin da ba su aikata ba, amma duk lokacin da rashin adalci mai girma irin wannan ya faru, wadanda ke da alhakin na gaskiya suna nan waje suna aikata wasu laifuffukan." Kamar yadda Gascon ya bayyana.
A cikin watan Fabrairun 2020, mutane 2,551 aka bayyana sako su a cikin rijistar kasa ta wadanda aka saka. Lokacin da wadannan mutane wadanda aka saki din suka kwashe a kurkuku da aka hada shi ya kama shekaru 22,540.
Post a Comment