Header Ads

Gwamnatin Zamfara ta baje kolin hujjojin yadda Matawalle ya yi walle-wallen biliyoyin nairori da sunan aikin filin jirgin sama


Gwamnatin Jihar Zamfara ta fito da sabbin hujjoji na yadda tsohuwar gwamnatin Bello Matawalle ta yi sama-da-faɗi da kuɗin aikin filin jirgin sama.

A Juma’ar da ta gabata ne Matawalle ya musanta zargin sace biliyoyin kuɗi da sunan aikin jirgin saman.

A wata takardar manema labarai, wacce Kakakin Gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris ya fitar ranar Litinin a Gusau, ta ce musanta wannan batu ba komi ba ne face rashin kunya da kuma kira wa kai fallasa.
Ya ƙara da cewa, idan ma dai ban da Matawalle na ƙoƙarin wawantar da mutane, ya manta yadda a ranar 25 ga watan Oktoba, 2021 ya kira waya ya bada umurni aka fitar da Naira biliyan 1 daga asusun Ma’aikatar Ƙananan Hukumomi, wanda a ciki ne aka tura wa ɗan kwangilar aikin filin jirgin sama Naira Miliyan 825.
 
Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Gwamnatin Jihar Zamfara ba ta yi niyyar tanka wa mutumin da ake zargi da satar dukiyar al’umma ba. Sai dai kawai don a fayyace tsakanin gaskiya da ƙarya, musamman ma ganin cewa ya fito ya musanta zargin da ake yi masa.
“Babu makawa, satar rashin imanin da aka tafka da sunan samar da tashar jirgin sama a Zamfara ba komi ba ne idan ka kwatanta shi da irin manyan sace-sacen da tsohuwar gwamnatin Bello Matawalle ta yi.

“Tsabar ƙarya ne a ce wai kuɗin da ‘yan kwangila suka gabatar da farko ya kai biliyan 28, amma tsohuwar gwamnatin ta zaftare shi zuwa biliyan 11. Babu wani ɗan kwangila da zai aminta a zaftare masa kuɗin aiki da kaso 61%, ba tare da asalin aikin ya taɓu ba. Wannan ya sa shakku a asalin aikin tun farko. Ko ba komi Matawalle ya fallasa mana nagartar ɗan kwangilar da suka kawo.

“Matawalle, ya yi iƙirarin cewa aikin na tashar jirgin sama wai an fara shi ne kan tsarin tallafin banki na ‘Contract Financing’. Wannan abin kunya har ina? Tsarin tallafin kuɗi da banki ke ba ɗan kwangila sunan sa ‘Contract Financing Facility’, shi kuma ana ƙulla shi ne tsakanin ɗan kwangila da banki, babu ruwan gwamnati a ciki. Don haka tsagoron ƙarya ce.

“Sannan batun wai kuɗaɗen da aka biya ɗan kwangilar an yi su bisa sahalewar Ma’aikatar Ayyuka, shi ma ƙarya ne. Hujjojin da muke da su, kuma waɗanda muka saki a yau sun tabbatar da an biya kuɗin ne ba tare da bin duk wata ƙa’ida ba.

“Ko don tarihi, ya na da kyau a sani cewa, an biya ‘yan kwangilar kaso 30% na aikin a matsayin biyan farko, inda aka ba su Naira 3,465,569,736.90, wato Naira biliyan 3.46, daga asusun Ma’aikatar Kuɗi ta Jiha, a ranar 19 ga Yuni, 2020.  

“A matsayin biya na biyu, an sake tura musu Naira biliyan 2, 310, 379, 824.60 daga asusun Ma’aikatar Kuɗin Jiha, a ranar 19 ga Yuni, da sunan bashi (wanda babu wannan tsarin sam a ƙa’idar gudanarwa ta gwamnati). 

"An sake tura masu Naira miliyan 825 daga asusun Ma’aikatar Kananan Hukumomi a ranar 25 ga Oktoba, 2021 a matsayin biya na uku. 

“Haka kuma batun da Matawalle ya yi na cewa ɗan kwangilar ya kammala wasu ayyukan da suka haɗa da hanyar tafiyar jirgi, magudanan ruwa, babbar ƙofar shiga tashar jirgin duk ƙarya ce. Shi ma akwai hotunan mun sake su.

“Iƙirarin wai an kammala wasu daga cikin ayyukan da kaso 50% zuwa 100% ma ƙarya ce. Ai filin jirgin na nan, duk wanda ke son gani da idon sa ya na iya zuwa don ganin irin ɓarnar da Matawalle ya yi.

“Hujjojin da muke da su sun tabbatar da cewa Hukumomin Kula da Filayen Jiragen Sama na Tarayya, irin su NCAA da NAMA duk ba a shigar da su cikin lamarin ba a farko, wanda ya saɓa da ƙa’idar gudanarwa ta sashen sufurin jiragen sama. 

"Da a ce da gaske tsohuwar gwamnatin Matawalle take da tun a wurin fitar da tsarin aikin filin jirgin saman za su nemi sahalewar waɗannan hukumomi.

“Muna so Matawalle ya yi wa duniya bayanin dalilin da ya sa ya biya ɗan kwangila zunzurutun kuɗi har Naira biliyan 6.78 kan aikin da su kan su sun tabbatar da cewa iyakar sa kaso 30%. Wanda kuma yanzu aka yi watsi da shi.

“Gwamnatin Dauda Lawal ba shaci-faɗi take fitarwa ba, hujjoji ne waɗanda kowannen su ke da takarda.

"Kwamitin Amsar Mulki ya yi dogon nazari kan hulɗoɗin gwamnati, wanda rahoton wannan kwamiti na da matuƙar tada hankali.

“Da sannu za mu fitar wa da al’umma irin satar rashin imanin da Matawalle ya jagoranta a tsohuwar gwamnatin sa. Kuma babu ko tantama cewa duk waɗanda ke da hannu a irin waɗannan ayyuka na almundahana da babakere ba za su sha ba. Wannan ba komi ba ne daga cikin abubuwan takaicin da za mu fallasa wanda tsohuwar gwamnatin ta aikata.” Cewar sanarwar da Suleiman Idris ya fitar.

No comments

Powered by Blogger.