Header Ads

Tinubu ya sadaukar da kai ga manufofin Nijeriya da Afrika a duniya – Minista

Alhaji Mohammed Idris a wajen walimar da aka yi a Ofishin Jakadancin Angola a daren Alhamis

Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa sadaukar da kai da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi bai tsaya ga Nijeriya kaɗai ba, har ma da dukkan nahiyar Afrika.
Ya ce: "Tun daga lokacin da ya kama aiki, an gan shi sosai a faɗin duniya ya na yayata manufofi da burukan Nijeriya da ma nahiyar Afrika."
Ministan ya faɗi haka ne a wurin wata walimar cin abincin dare wadda Ofishin Jakadancin ƙasar Angola ya shirya a Abuja a ranar Alhamis.

Ya ƙara da cewa Shugaba Tinubu ya na da shauƙin ganin ya inganta mu'amalar da ke tsakanin Nijeriya da sauran ƙasashen Afrika, ciki har da Angola.
Idris ya ce yanzu ana kallon Shugaban Ƙasa a matsayin uba a faɗin Afrika, wanda ke jagorantar ƙasar da ta fi kowace yawan jama'a da ƙarfin arziki a nahiyar.

A cewar sa, wannan ne ya sa aka naɗa Tinubu shugaban ƙungiyar ƙasashen Afrika ta Yamma, wato ECOWAS, jim kaɗan bayan an rantsar da shi a matsayin shugaban ƙasa.
Ya ce: “A jawabin sa a wajen babban taron farko da ya halarta na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNGA) a watan jiya, ya yi magana mai gamsarwa ƙwarai kan dalilan da su ka sa Afrika ta ke buƙatar sauran ƙasashen duniya su yi mata adalci, da abin da ya sa cigaban duniya ya na tattare ne da cigaban Afrika.
Ya ce, “Wato dai manufa, idan har duniya ta ɗauki batun samun cigaba da gaske, to tilas ne kuma ta ɗauki batun cigaban Afrika da gaske."
Ministan ya ƙara da cewa mafarkin Shugaba Tinubu da burin sa su ne ƙasashen Afrika su haɓaka dangantaka mai zurfi da ƙarfi a tsakanin su wanda "zai ba da dama ga nahiyar ta samu matsayi da ya fi na da girma da ƙarfi a fagen duniya da kuma samun dama mafi girma wajen samun 'yanci mai ɗorewa da arziki. Duk abin da ya gaza kan wannan, to ba za mu yarda da shi ba."
Ya yi la'akari da cewa idan har ba a haɗa kafaɗa aka yi mu'amala da haɗin kai tare ba, Afrika ba za ta cimma nasarar warware matsalolin ta ba.
Idris ya ce: "Ƙoƙarin magance ɗimbin ƙalubalen da ke fuskantar nahiyar a wannan zamani - irin su rashin tsaro, fatara, rashin aiki, labarai marasa daɗi, ƙarancin hada-hadar kasuwanci a tsakanin nahiyoyi, da sauran su - duk ya na buƙatar yin aiki kafaɗa da kafaɗa a matakin yanki da na nahiya baki ɗaya.
“Duk da yake akwai bambance-bambancen harsuna da al'adu da tsarin zamantakewar al'umma da na siyasa, tilas ne mu samo hanyoyin da za mu amince da su domin gabatar da matsaya ɗaya kan al'amurran da su ka shafi mu su waye a matsayin nahiya, da abin da mu ke so mu cimmawa a dukkan ɓangarori na rayuwa.
“Tilas mu haɗu mu tattaro tunani kan batun cigaban ƙasa, kafa masana'antu, cinikayya, samar da aikin yi, da kuma matsayin nahiyar mu a ƙarni na 21. Yanzu haka an yi nisa wajen aiki kan hakan, don a fitar da matsaya ɗaya haɗaɗɗiya wadda za a yi aiki da ita a matakai daban-daban."

No comments

Powered by Blogger.