Header Ads

Gwamna Abba Yusuf ya taya Sanata Kwankwaso murnar cika shekaru 67

Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano, ya taya tsohon Gwamnan Kano, jagoran Kwankwasiyya kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na NNPP a zaɓen 2023, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, murnar cikar sa shekaru 67 a duniya.

Cikin wata sanarwar mai taken: Taya *Madugu* *Uban* *Tafiya* Murnar Cika Shekara *Sittin* *da* *Bakwai*, wadda Kakakin Gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a safiyar Asabar, 21 ga Oktoba, Gwamna Abba ya jinjina wa Kwankwaso bisa kishin al'umma, jagoranci nagari da aiki tuƙurun da ya yi fice a kai.

"A madadin al'ummar Jihar Kano, *Mai* *Girma* *Gwamna*, *Alhaji* *Abba* *Kabir* *Yusuf* na cike da farin cikin taya shugaban mu, madugun mu kuma hasken fitilar mu, *Mai* *Girma* *Sanata* *Injiniya* *Rabi'u* *Musa* *Kwankwaso* PhD, FNSE, murnar cika shekaru 67 masu albarka a duniya."

Abba ya jaddada cewa Kwankwaso mutum ne nagari, mai aƙida ta ƙwarai, juriya da hangen nesa. 

"Kyakkyawar aƙidar ka ta gina al'umma, babban misali ne abin koyi ga dukkan shugabannin wannan zamani.

"Nasarorin da ka cimma da ayyukan da ka aiwatar sun tabbatar da kyakkyawar aƙidar ka ta kishin al'umma da tsayin-daka kan nagartacciyar turbar siyasa, domin sadaukar da kai ga jihar mu da ƙasa a kowane lokaci."

Daga nan sai gwamnan ya yi addu'a Allah ya ƙara wa Kwankwaso lafiya da ƙarfin hali da hikimar ci gaba da yi masu jagoranci, har ya dangana ga ƙololuwar nasara nan ba da daɗewa ba.

No comments

Powered by Blogger.