Header Ads

Me ya sa Atiku ke neman takardun Jami'a na Tinubu?


Jama'a da dama sai tambaya suke yi, shin me ya sa Alhaji Atiku Abubakar ke neman ganin takardun kammala Jami'a na shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu?
Ɗan takarar shugaban kasa na PDP Alhaji Atiku Abubakar ya buƙaci samun takardun ne don amfani da su a kotunan Najeriya wajen tabbatar da hujjarsa cewa takardun Tinubu na jabu ne.

Wata kotu a Amurka ta umurci Jami’ar Jihar Chicago da ta bai wa Atiku Abubakar damar ganin takardun karatun Shugaban Najeriya Bola Tinubu.

Alkaliyar kotun, Nancy Maldonado, ta yi watsi da buƙatar Tinubu na kin amincewa Atiku ya ga takardun, inda ta ba da wa'adin kwanaki biyu ga Jami'ar don miƙa wa Atiku takardun.

Ta kuma amince da hukuncin da alkalin wata kotun majistre a Amurka, Jeffery Gilbert ya yanke a ranar 20 ga Satumba, wanda ya umarci Jami'ar ta Chicago da ta saki takardun karatun Tinubu kamar yadda Atiku ya buƙata, inda ta jaddada cewa Atiku yana da damar samun takardun.

A cewar alkaliyar, dole ne Jami'ar ta kammala duk wani abu da ya kamata don sake takardun nan da ranar Talata.

Idan za a iya tunawa, É—an takarar shugaban Ć™asa a babbar jam’iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakara, ya garzaya wata kotu a Amurka domin ta tilasta wa jami’ar Chicago ta saki takardun karatun Tinubu, domin hakan zai ba shi damar kalubalantar zaÉ“en shugaban Ć™asa na ranar 25 ga watan Febrairu.


No comments

Powered by Blogger.