Header Ads

Ƙungiyar kwadago ta ƙasa ta bayyana fara yajin aiki a ƙasa baki daya daga ranar Laraba mai zuwa

Wasu 'yan kungiyar kwadago ta NLC

Kungiyar kwadago ta kasa (NLC) ta bayyana cewa za ta fara yajin aiki a kasa baki daya daga ranar Laraba mai zuwa.

Wannan na zuwa ne a yayin da ake tsaka da fuskantar karancin mai biyo bayan jawabin rantsuwa da Tinubu ya gabatar inda ya ciki ya bayyana cewa "tallafin mai ya wuce." 

Shugaban kungiyar NLC, Joe Ajaero, ne ya bayyana haka bayan taron gaggawa da majalisar zartarwa ta kasa (NEC) ta kungiyar ta gabatar a Abuja.

Ya bayyana cewa gwamnati, musamman kamfanin mai na kasa (NNPC) na da daga yanzu har zuwa Laraba mai zuwa domin dawo da tsohon farashin man (PMS).

Ajaero ya bayyana cewa kasawar gwamnati na mayar da tsohon farashin zai haifar da zanga-zanga a fadin kasa baki daya.

A ranar Laraba, awowin da aka yi ana tattaunawa a tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar ta NLC a kan al'amarin sun kawo karshe ba tare da cimma wata matsaya ba. 

Wakilan gwamnatin tarayya sun hada da Dele Alake, kakakin shugaban kasa Bola Tinubu; babban shugaban sashen zartarwa na hadakar NNPC, Mele Kyari, gwamnan babban bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele; da kuma tsohon gwamnan jihar Edo, Adams Oshiomhole. 

A bangaren kungiyar kwadago, akwai shugaban kungiyar Joe Ajaero; da kuma shugaban kungiya kwadago ta Nijeriya (TUC), Festus Osifo.

NLC ta nemi gwamnatin tarayya ta maido da yadda al'amurra ke tafiya a baya ta hanyar maido da farashin da ke nan a baya kafin ta cigaba da tattaunawa da kungiyar.

Ajaero ya kafe cewa gwamnatin tarayyar ba ta fara wata tattaunawa ta daukar matakin kawo sauki ga 'yan Nijeriya ba, wani dalili na yin watsi da sanarwar ta bayan nan.

No comments

Powered by Blogger.