Amurka za ta gina cibiyar yanki-yanki ta hukumar CIA a Lebanon - Rahoto
Amurka na aiki kan gina cibiyar yanki-yanki ga hukumar leken asiri ta Amurka (CIA) a Lebanon, a cikin babbar harabar ofishin jakadanci da ke da fadin mita 93,000 a kan kasa mai fadin hekta 27 (kadada 64) a babban birnin kasar, Beirut, kamar yadda majiyoyin tattara bayanan sirri suka bayyana a ranar 29 ga watan mayu.
Kamar yadda kafar watsa labaru ta Teghrib News Agency ta ruwaito, majiyoyin sun bayyana cewa hukumar tattara bayanan sirri ta Amurka na kallon Lebanon a matsayin wurin da ya fi tsaro kuma muhimmin yanki na ajiye jami'an tattaro bayanan sirri.
Bayan haka, Washington ma ta na da niyyar amfana daga hadakar tattara bayanan sirri da ta kware da kuma sashen tattara bayanan sirri na hukumar sojojin Lebanon, B2, kamar yadda majiyoyin suka bayyana.
Sashen yanar gizo na kasar Faransa ya samu bayanin cewa samar da kudade da Amurka ke yi ga sojojin Lebanon ya hada da tabbacin kyale hukumar tattara bayanan sirri na tsaron Amurka (DIA) samun dama mara iyaka kan bayanan sirrin ta.
Post a Comment