Header Ads

Majalisar wakilan Nijeriya ta bukaci Tinubu da ya sa dokar ta ɓaci kan shaye-shaye a Nijeriya

Majalisar wakilan Nijeriya ta bukaci shugaban kasa, Bola Tinubu, da ya sa dokar ta baci kan shaye-shaye a kasar.

Wannan ya biyo bayan wani kuduri ne na gaggawa da ke da matukar muhimmanci ga kasa daga daya daga cikin mambobin majalisar, Francis Agbo, wanda ya jawo hankalin majalisar kan kokarin da hukumar hana sha da tu'ammali da miyagun kwayoyi a Nijeriya (NDLEA) ke yi wajen kawar da miyagun kwayoyi a kasa.

Majalisar ta ma nuna damuwarta kan irin kayayyaki da makaman da hukumar ta NDLEA ke da su, inda ta nemi da a kara kudaden da ake ware ma hukumar a kasafin kudi.

'Yan majalisar dokokin na so a rinka ba hukumar ta NDLEA kudi ne kai tsaye daga sashen shugaban kasa.

Majalisar wakilan ta 9 za ta gabatar da zaman ta na ban kwana a ranar Talata, 6 ga watan Yunin shekarar 2023.

No comments

Powered by Blogger.