Header Ads

Sakin takardun karatun Tinubu: Ko hakan zai taimaki ƙarar da Atiku ya shigar?

Tinubu da Atiku

Jami'ar Jihar Chicago da ke Amurka ta saki takardun karatun Shugaba Bola Tinubu. Sai dai tambayar da jama'a ke yi ita ce hakan zai taimaka wa Atiku na PDP kuwa?

Tambari da kuma bajon da jami'ar CSU ta saki na digirin a 1977 sun yi daidai da irin wanda Shugaba Tinubu ya gabatar wa INEC, sai dai an samu banbanci a kwanan wata.

Sai dai cikin bayanin da jami'ar ta yi, ta ɗauki alhakin kuskuren da aka samu a kwanan watan, tana cewa kuskure aka samu wajen rubutawa.


Wannan biyo bayan da ɗan takarar shugaban ƙasar a a 2023 ƙarƙashin jam'iyyar PDP Atiku Abubukar ya buƙaci hakan ne.

A ƙarshen makon da ya gabata ne, wata kotun gunduma da ke arewacin Illinois a Amurka ta bayar da umarnin a sakarwa Atiku takardun karatun Tinubu.

A wani martani na buƙatar da Atiku ya miƙa a karo na uku, wanda ya nemi a saki kwafin sakamakon digiri 1977, Jami'ar ta ce takardun sun yi daidai da na Tinubu da ke ɗauke da kwanan watan 27 ga watan Yunin 1977.

"Bayan bincike mai zurfi, Jami'ar CSU ta gano ta kuma gabatar da takardun da aka nema kuma ta gabatar da su don amsa wannan bukatar. Lambobin takardun su CSUO008 zuwa CSU0010.

"An shafe sunayen ɗaliban da ke kan takardun saboda a sakaya sunansu.

"CSU za ta kuma saki sakamakon daliban da suke kusa da shi, masu lamba CSU0011 da lamba 0017 na wasu ɗaliban bayan an doɗe sunayen (saboda a sakaye sunanyensu)”.

"Waɗannan takardun sun yi daidai da yadda na Tinubu, dalibin da aka yi wa sauyin makaranta yake," kamar yadda jami'ar ta rubuta.

A baya Tinubu ya yi iƙirarin ɓatan ainihin takardunsa na jami'ar, abin da ya sa ya gabatarwa da hukumar zaɓe INEC wata takardar a matsayin madadin takardun na ainihi domin takarar shugabancin Najeriya a 2023.

Takardu da dama na waɗari a kafafen sada zumunta a matsayin shaidar kammala karatun na Tinubu a Jami'ar jihar Chicago.

A ranar 19 ga watan Satumba ne, Jeffrey Gilbert na kotun majitare da ke Amurka ya amince da buƙatar da aka shigabar gaban kotun tare da ba da umarnin sakin takardun karatun Bola Tinubu cikin sa'a 24.

A wani ƙoƙari na ganin haka bai faru ba, Tinubu ya ɗaukaka ƙara kan wannan umarni.

Nancy Maldonado ta kotun tarayya ta sake tabbatar da wannan hukunci da Tinubu ya so ƙalubalanta, inda ita ma ta ce a saki takardun.

Domin bin umarnin kotun da cika buƙatar Atiku Abubakar CSU ta ce ba za ta iya nemo ainihin kwafin takardun da ta bai wa Tinubu ba 1979.

"A tsarin CSU ba ta ajiye kwafin takardun ɗaliban da suka yi digiri, kuma bayan dogon bincike ta gaza samo kwafin irin wanda ta bau wa Tinubu a 1979, don haka ba a samu takardun da aka buƙata ba," in ji jami'ar.

Sai dai jami'ar ta saki takardun wasu ɗaliban da ta rufe sunayensu, waɗanda suka yi daidai da na Tinubu domin tabbatar da cewa ya kammala makarantar a baya.

Atiku Abubakar dai na son amfani da takardun ne a matsayin shaida a kotun ƙolin Najeriya kan ƙorafin da ya shigar game da sakamakon zaɓen shugaban ƙasar da aka yi a 2023.


No comments

Powered by Blogger.