Header Ads

'Yan jarida sun cancanci samun rayuwa mai inganci a Nijeriya - Idris

Alhaji Mohammed Idris, Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa 'yan jarida a Nijeriya su na aiki a cikin mawuyacin yanayi, kuma sun cancanci samun ingantacciyar rayuwa, yadda za su samu damar gudanar da ayyukan su cikin sauƙi da walwala.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris ne ya bayyana haka a wata tattaunawa da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN), a Abuja.

Idris ya ce wasu 'yan jaridar ma sun rasa rayukan su wurin aikin su. A kan haka ya ce zai yi iyakar ƙoƙarin sa domin inganta rayuwar 'yan jarida a gwamnatance.

"Za mu yi ƙoƙarin ganin ana bai wa 'yan jarida dukkan haƙƙoƙin da su ka cancanta a ba su.

"Saboda su na aiki a cikin mawuyacin yanayi, wani lokaci ma har rasa rayukan su su ke yi, kamar yadda jami'an tsaro ke rasa na su rayukan wajen tabbatar da tsaro.

"Sau da yawa za ku ga 'yan jarida kafaɗa-da-kafaɗa a cikin jama'an tsaro idan sun fita yaƙi da ta'addanci. Da dama a cikin su kan koma gida da raunuka a jikin su.

"Kuma kun dai ga yadda ɗan jarida ya rasa ran sa a Zamfara saboda hare-haren 'yan bindiga.

"To duk irin waɗannan ba abubuwan jin daɗin ba ne a ce a matsayi na na Ministan Yaɗa Labarai na faruwa. Ina so na ga ƙarshen wannan matsalar.," inji Idris.

Sannan kuma ya kawo hanzarin dalilin da ya sa gwamnati ba za ta tsame 'yan jarida ta yi masu ƙarin albashi su kaɗai ba. Ya ce akwai muhimmancin a duba ainihin yadda aikin na su ke da tasiri da haɗari, domin a magance matsalolin da su ke fuskanta.

"Ni a sahun gaba na ke na masu hanƙoron ganin rayuwar 'yan jarida ta inganta. Kuma ina taka-tsantsan da sanin cewa su na aiki ne cikin da'irar iyakar gejin tattalin arziki ƙasar mu.

"Don haka ya zama tilas mu dubi wannan lamari baki ɗaya, domin a ƙarshe a yi mana kyakkyawar shaidar 'yan ƙasa nagari."

No comments

Powered by Blogger.