Header Ads

Nijeriya ta tabbatar wa Amurka da ci gaba da yin riƙo da 'yancin 'yan jarida


Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ƙara tabbatar wa da gwamnatin Amurka cewa Nijeriya na kan turbar da ta ke a kai ta yin riƙo da 'yancin 'yan jarida da kafafen yaɗa labarai.

Ya ce akwai buƙatar wannan 'yanci sosai domin ta hanyar kafafen yaɗa labarai ne dimokiraɗiyya ke ka ƙara karsashi, tasiri da nagarta a cikin zukatan al'umma.

Hakan ya na ƙunshe ne a cikin wata sanarwar da mataimaki na musamman a fannin yaɗa labarai ga ministan, Malam Rabi'u Ibrahim, ya fitar a ƙarshen makon jiya.

Ministan ya bayyana haka a lokacin da Babban Jami'in Amurka mai Kula da Al'amurran Nijeriya, Mista David Greene, ya kai masa ziyara cikin makon jiya.

Ya ce: "A yayin da mu ke goyon baya da ɗabbaƙa 'yancin kafafen yaɗa labarai da na 'yan jarida, mu na kuma yin kira ga gwamnatin Amurka da ta ba mu goyon baya ta hanyar ƙara zurfafa horaswa ga 'yan jarida, musamman a fannin binciken tabbatar da gaskiya da fayyace sahihin labari daga labaran bogi."

Idris ya ƙara da cewa, "Yin hakan zai ƙara rage yawan watsa labaran bogi, bayanan karkatar da hankalin jama'a, da rage bazuwar ji-ta-ji-ta a cikin jama'a."

Ministan ya jaddada aniyar da Nijeriya ta sa a gaba wajen ƙara wa dimokiraɗiyya daraja da ƙima, ya na mai cewa, "Muhimmin abu ne a matsayin Amurka na babbar ƙawar Nijeriya ta ƙara zurfafa goyon bayan ta ga gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, a ƙoƙarin da gwamnatin ke yi na bunƙasa tattalin arzikin ƙasar nan."

A jawabin sa, Mista Greene ya ce Amurka na goyon bayan Nijeriya ɗari bisa ɗari wajen inganta dimokiraɗiyya da inganta ayyukan kafafen yaɗa labarai.

Ya ce an keto shekaru da dama ƙasar sa ta na bayar da guraben ƙaro ilmi, bada horaswa da kuma fannin inganta tsaro.

No comments

Powered by Blogger.