Header Ads

RESOURCE FORUM KATSINA SUN GUDANAR DA TARON FAƊAKARWA AKAN ABINDA KE FARUWA A FALASƊIN.


Daga:- Muhammad Ali Hafizy.

A ranar Asabar 25/11/2023 ne,  ’yanuwa Musulmi almajiran Shaikh Ibrahim Zakzaky (H) "Resource Forum" na yankin Katsina suka gabatar da faɗakarwa akan abinda ke faruwa a falasɗin.

Taron ya samu halarta mutane daga ɓangarori daban daban wanda ya haɗa da Shi'a da Izala da Ɗarika da kuma Cristian.

An fara gudanar da taron ne da misalin ƙarfe 11 na safiyar ranar, inda aka buɗe taro da Addu'a sannan akayi karatun al'ƙurani mai girma sannan aka gabatar da maƙasudin taron.

Dr. Abdullahi ’Yar'adua shi ne shugaban makarantar (Fudiyya Secondary School Allience) dake cikin garin Katsina. Shi ne wanda ya fara jawabi a muhallin ya gabatar da maudu'i mai taken (Abinda ke faruwa a Falasdin) Dr. Abdullahi yayi jawabi sosai akan asalin faɗan dake tsakanin Falasɗinawa da kuma Isra'ila. 

“An fara faɗa tsakanin Yahudawa da Falasɗinawa tun a shekarar 1897 da wasu mutane da ake kira "Zionist" suka bukaci a samar masu da ƙasar da zasu zauna a cikin kasar Falasɗinu.” yace asalin rigimar kenan.
Dr. Abdullahi ’Yar'adua ya bayyana ƙasashen da suka bada gudumawar su wajen ganin an samar masu (Zionist) da mazauni da ƙarfi, inda yace ƙasashe Ingila, Amurika da Faransa, inda yace Kasar Ingila itace ta Ayyana samar da kasar Israel a cikin kasar Falasɗinu inda wannan bukata ta kasar Ingila ta samu amincewar Majalisar Dinkin Duniya a shekarar 1947. Daga nan ne asalin faɗan ya soma.

Sannan aka bukaci shima Dr. Abdullahi Isa (Malami a Makarantar Hassan Katsina Pholytecnic) ya gabatar da maudu'i mai taken "Danniya da Zaluncin da ake ma Falasdinawa"

Dr. Abdullahi Isa, ya kawo tarihin yadda Yahudawa suka haɗa kai suka ƙirƙirar ma Israel ƙasa a lokacin da (Hitila) ya tarwatsa su. Dr Abdullah Isa yace " Shi Hitila ya san irin makircin da Yahudawa suke dashi shiyasa ya yake su har ya tarwatsa"

Dr. Abdullahi Isah ya ƙara da cewa "Bayahude yana so ya mamaye Duniya ne, yace dama yankin yammacin Duniya suke dashi, amma a haka saida suka shigo yankin Larabawa, da Afrika ta hanyar shigar da jininsu a jikin Sarakuna, Malamai, da duk wasu da suke saran zasu iya amfani dasu don yakar al'ummar yankin," yace "Ba abin mamaki bane don kaji bakar fata yana goyon baya ko yana yin aiki irin nasu, domin akwai bakaken Yahudawa a cikin mu" 
Sannan ya taɓo irin yanayin da muka tsinci kanmu a yanzu, ta fuskacin rarrabar kawukan mu, da rushewar tattalin arzikin mu, yace "Duka wannan yana daga cikin shirin Yahudawa na gurin mallakar Duniya baki ɗaya" 

Shaikh Isma'il Bin Zakariyya Alkashnawy yana ɗaya daga cikin Malamin Addinin Musulunci a garin Katsina, ya yi jawabi akan wasu Ayoyin Alƙur'ani Mai girma guda huɗu da suke magana akan Yahudawa, inda a ciki ya faɗakar, ya kuma tunasar dangane da Sharrinsu, Butulcinsu, da Makircinsu, yace "Duk da a cikinsu akwai mutanen kirki, amma ba a taɓa wata halitta da tayi ma Allah Butulci ba kamar Yahudawa, yace shiyasa Alƙur'ani mai girma ya fallasasu ya kuma tona masu asiri”.

Sannan ya yi fatan Alkairi ga Shaikh Ibrahim Yakub Zakzaky (H) da addu'ar Allah ya bashi lafiya, da kuma Addu'a ga Shaikh Yakub Yahaya Katsina.

Madam Martha Cosmas Essien ɗaya daga cikin mahalarta taron ta bayyana damuwar ta tare da juyayi akan halin da Falasɗinawa suke ciki na irin Zaluncin da ake masu tare da yin Addu'o'i na musamman garesu.

Daga ƙarshe wakilin Shaikh Yakub Yahya Katsina, Malam Shehu Usman Dalhatu Ƙarƙarku shi ne ya gabatar da jawabin rufe taron, sannan Malam Ali Hafizy ya jagoranci gabatar da Addu'a ta musamman ga Falasɗinawa.
Sannan aka sallami mahalarta taron.

No comments

Powered by Blogger.