Header Ads

WACECE TA DACE NA AURA.?




Fatima Adamu Tinja, Fika


Babban burin kowane Namiji shi ne samun Mace ta gari. A kullum tsakanin Mata da Maza addu'ar su da ta masoyansu in ana batun abokin zama to babban fatan shi ne samun abokin zama nagari. Amma da dama masu neman wannan abokin zaman na kwarai basu damu da su zama na garin ba.

To abin daurin kai shi ne, ta yaya za a samu wannan hadin na iyalai masu daraja in har halayensu bai zo daya ba?

A rayuwar aure kowa da irin hakki da kason nauyin da yake dauka. Namiji kan zama ginshiki mai tsawatarwa da shiryarwa da sa ido da sauran nauye-nauye narayuwar iyalinsa. Inda mace kuma ke kula da gida ta kula da Mijin, ta gyara, ta inganta alakarsa da iyaye ‘yan'uwansa. In an samu zuriya ta kula da ingancin walwalarsu da tarbiyyarsu.

Hatta mu'amalar mijin ta kasuwa ko office da nutsuwarta ya ke samun nasara. To in kuwa haka ne, to waya fi dacewa da ya zamo na gari da farko? 

Ko wane dan Adam yana da burin ya zabi mace ta gari ko da kuwa shi ba namiji na gari bane domin kowa ya yarda cewa mace ta gari alheri ce ga mijinta. 

Kamar yadda yazo a hadisin Manzon Allah (S) Cewa; Duniya gidan jin dadi ce, amma mafi alhairin abin jin dadin duniya ita ce mace ta gari.

Manzon Allah(S) Yace; "Ana auren mace dan abubuwa guda 4, sune, KYAU, DUKIYA, NASABA, ADDINI. Sai yace; Amma ina kwadaitar muku da ku auri me ADDINI.

To amma sai ya zamana wasu daga cikin Mazajenmu na yanzu, sun fiye maida hankulansu wajen zabar Mace mai DUKIYA, NASABA, da kuma KYAU. Sun bar mai ADDININ, wanda Manzon Allah (S) ya kwadaitar gare su da su auresu.

Sai dai kuma abin da basu gane ba shi ne, matukar ka auri Mace, dan DUKIYARTA to bai zama lallai ka ci moriyarta da ranta ba, bare bayan ranta, dan ba ko wane me kudi ne ke taimakon sirikinsa ya masa hanyar arziki ba, kuma ma da za kayi hakuri arzikinka na bibiye da kai kamar yanda ajalinka ke bibiyarka, lokaci kawai yake jira.

Sannan koda ka zai zama kai da gidanka, amma ta fika iko da gadara da gidan, har ma yazama kamar ita ce mijin kaine matar, gadararta ka aureta ne dan dukiyarta. Dan'uwa ina so ka sani cewa, ita dukiya zata iyakarewa ta barka.

MACE MAI NASABA. Babban burinka ka auri mace me Nasaba. Ace wance ‘'Yar wane, jikar wane, kai shi ne burinka da jin dadinka. Ita kuma tana ganin cewa masu sha'awar aurenta 'yan neman suna ne da son alfarma, sai kayi abin da kake so a ganinka zata zame maka garkuwa.

To bari kaji, iyakaci kaci albarkacinta alokacinda take da rai ne kadai, kuma ita dai 'yar dangi har gara Mata masu dukiya da ita, domin mai yiwuwa a cikinsu a samu wanda zasu bar SADAKA. Sannan itama za'a iya wayan gari ya zama bata da kowa nata, duk sun mace, Allah ya rufa asiri.

MACE KYAKYKYAWA


Da yawan maza sun fi son Mace fara kyakkyawa. To ga shi dai maza sunfi Sha'awarta, amma sam-sam babu wani abin amfana a tare da'ita. Watakila ace ta haifi 'ya'ya kyawawa, gashi ta haifo su da kyau kuma babu tarbiyya, sun zama fitina ga al'umma, to yanzu ina riba a nan ?

Har gara 'yar dangi da ita, dan kila ita riba ce, ba za a samu daga wajenta ba, amma ita nakasu ce za a samu a tare da ita, domin zama da ita fitina ne da kuma damuwa, idan har bata da tarbiyya.

Ina so mu sani cewa; shi kyau yana iya gushewa ta hanyoyi da yawa, yana iya yiwuwa tsautsayi ya iya fadawa kan wannan kyakkyawan fuskar da surar ta ta, har ya zama kyan na ta ya baci.

Sannan akwai tsufa, akwai mutuwa, domin idan ta rasu, duk farin fatarta, da tsawon gashinta da hancinta da kuma surarta, haka za a binne ta da kayanta, tunda dai ba za a ciri kyan nata amanna maka shi agoshinka ko ‘ya’yanka da sunan gado ba.

MACE MAI ADDINI.

Ita ce wacce Manzon Allah (S) ya kwadaitar da asame ta amatsayin matar aure. Domin ta tattara abubuwa da yawa; ILIMI, WAYEWA, HANKALI, NUTSUWA, da sauransu. Amma a nan kuma ana amfana da ita ko da ta rasa wadancan ababe, (KYAU, DUKIYA, NASABA), sai tafi soyuwa a wurin Allah, tafi soyuwa a wurin halittunsa na sama da kasa.

"Shi dai Allah ba ya duba zuwa ga halittarku yana duba ne zuwa ga zukatanku" inji Manzon Allah(S).

Su kuwa bayin Allah sun fi son zama da son jin motsin wanda suke karuwa dashi. Ilimin da ta bayar ba ya taba lalacewa, dan idan ta koyawa ma wani, shima zai koya ma wani. To da haka za'aita tafiya, mun ga kenan ko a nan ma ta bada gudumawarta ga al'umma ba ga 'ya'yanka kadai ba.

Ya kai dan'uwa me daraja, ka sani hakki ne a kanka kanemar wa 'ya'yanka uwa ta gari, babu wacce tafi cancanta da hakan illah mace ta gari, mai addini.

No comments

Powered by Blogger.