Header Ads

Ambaliya: Mun kai kayan agaji a jihohi 21 – Minista Sadiya

 Wasu ma'aikata na raba kayayyakin agaji ga wadanda ambaliya ta shafa

Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta bayyana cewa ma'aikatar ta rarraba kayan agaji ga dukkan jihohi 21 da bala’in ambaliyar ruwa ta shafa a sassa daban-daban na ƙasar nan a bana.

Ministar ta bayyana hakan ne a wajen taron da ta yi da manema labarai a ranar Talata a ofishin ta a Abuja domin bayyana irin ayyukan jinƙai da ma’aikatar, tare da haɗin gwiwa da Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa (NEMA), su ka kai a wuraren da ambaliyar ta shafa.

Ministar ta ce, “Zuwa yanzu jihohi 21 sun karɓi nasu kayan agajin, waɗanda su ka haɗa da Abiya, Adamawa, Anambara, Bayalsa, Ekiti, Inugu, Imo, Jigawa,
Kaduna, Kano, Kwara, Legas, Nasarawa, Neja, Ogun, Ondo, Oyo, Sakkwato, Taraba, Yobe da Gundumar Birnin Tarayya.”

Hajiya Sadiya ta ce sakamakon bala'in ambaliyar, kimanin mutum 1,427,370 su ka rasa matsugunan su, wasu 612 kuma su ka rasa rayukan su, sannan wasu 2,776 su ka samu raunuka.

Ta ƙara da cewa yanzu haka akwai ƙwararru da ke gudanar da irin waɗannan ayyuka, musamman ganin cewa har yanzu akwai wasu Ƙananan Hukumomi da ba sa shiguwa saboda matsalar ambaliyar.
 
Ta ce: “Domin samun nasarar wannan aiki, mun haɗa hannu da sashen kai agaji na sojojin ƙasar nan, tare da sauran ƙwararru da ingantattun kayan aiki, domin amfani da su wajen isa ga wurare masu wuyar zuwa da kuma jama’ar da ke cikin haɗari.” 

Ministar ta ba da tabbacin cewa har yanzu ana ci gaba da wannan aiki na kai kayan agaji ga jihohin da wannan ambaliya ta shafa.

Yayin da ta ke ƙarin haske game da kayan da ma’aikatar ta raba, ministar ta ce, “Abubuwan da mu ka raba, kaya ne na buƙatar gaggawa na abinci, waɗanda su ka haɗa da shinkafa, masara, garin rogo, man gyaɗa, wake da kayan dafa abinci.

"Kayan da ba na abinci ba kuma da aka kai domin samun matsuguni na wucin-gadi ga jama'ar da su ka rasa wurin zama sun haɗa da kwanon rufi, siminti, kusoshi, sili, barguna, tabarmin roba da kwano.”

Haka kuma ministar ta ce ma'aikatan ceto su na nan su na aiki wurjanjan tun da aka fara ambaliyar, su na kwashe wadanda bala'in ya shafa tare da sama masu matsuguni, kuma ana kai wasu asibiti domin su samu kula ba tare da bata lokaci ba.

Ta yi kira ga sauran masu ruwa da tsaki a lamarin da su shigo cikin ƙoƙarin da ake yi na taimaka wa  wadanda abin ya shafa. Ta ce, “Fatan mu shi ne sauran ma'aikatun gwamnati irin su Ma'aikatar Albarkatun Kiwon Lafiya,  Ayyuka da Gidaje, Aikin Gona, da Yanayi za su zo mu hada gwiwa a taron manema labarai na gaba  domin su ma su gabatar da nasu bayanan kan ayyuka su domin mu yi bayani kan wannan aikin agaji da mu ke yi.

“Ina yin kira kuma ga gwamnatoci a kowane mataki, musamman na jihohi da ƙananan hukumomi, da su ba 'yan sanda da mu bayanan da su ka dace, sannan su taka rawa wajen aikin ceto, kamar yadda Tsarin Gaggawa kan Shirya wa Ambaliya da Ceto na Kasa ya tanadar, wato 'Flood Emergency Preparedness and Response Plan'.

“Ina jinjina wa jama'ar garuruwa saboda dagewar su. Mun samu rahoton cewa a cikin ƙananan hukumomi 144, jama'a a garuruwa sun yi aiki tare wajen samar da agajin farko ga iyalan su da maƙwatan su.

“Tawagar masu aikin bincikowa da ceto jama'a, waɗanda aikin ɗauko jama'a da ba su agajin farko don ceton rayuwar su tare da ba su magani da takardar zuwa asibiti ya rataya a wuyan su, ya zuwa yanzu sun isa yankunan ƙananan hukumomi 199 a jihohi 25.

“Ana ci gaba da aiwatar da waɗannan ayyuka kuma ina kira ga jama'ar garuruwan da ke cikin haɗarin aukuwar bala'i da su tabbatar da sun bi gargaɗi da umarnin  da waɗannan ma'aikatan su ke ba su domin su na aiki ne saboda su kare tare da ceto rayuka.

Ministar ta mika Godiya ga Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari saboda “goyon bayan da ya ba mu tare da ɗaukar mataki da sauri wajen magance matsalolin ambaliya.”

Ta ƙara da cewa: “Wata babbar tawaga za ta ziyarci wasu daga jihohin a makon gobe domin  ɗorawa kan ayyukan ceto da agaji tare da gano sababbin matsaloli  da kurakurai a ayyukan waɗanda ke bukatar a gyara su. Hakan zai ba gwamnati damar nazartar al'amarin a kurkusa tare da haɗuwa da waɗanda abin ya shafa da iyalan su.”
Wani wuri da ambaliyar ruwa ta shafa

No comments

Powered by Blogger.