Header Ads

Zaɓen 2023: Za mu hana maguɗi ta hanyoyi 4, inji INEC


Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta cewa akwai wasu manyan matakai guda huɗu da ta samo waɗanda za su hana wani ya bi wata hanya ya yi maguɗi an zaɓen 2023.


Mataimakin Sakataren INEC, Injiniya Chidi Nwafor, shi ne ya fadi haka lokacin da ya ke magana a wurin taron zaburar da matasa kan muhimmancin zaɓe, wanda ƙungiyar Yiaga Africa ta shirya a Inugu.

A cewar sa, mataki na farko shi ne dabarar tantance wanda ya yi rajistar mallakar katin zaɓe sau biyu ko fiye da haka, wato 'Biomodal Voter Accreditation System' (BVAS).

Na biyu shi ne amfani da na'urar tantance adadin masu zaɓe a rumfunan zaɓe, wato 'INEC Voter Enrollment Device' (IVED). Shi wannan tsari ya na maganin masu satar ƙuri'a ko ɓarayin akwatin zaɓe.

Na uku shi ne manhajar tattara sakamakon zaɓen da kowa zai iya gani ido-da-ido, wato 'INEC Result Viewing Portal' (IRVP).

Mataimakin sakataren ya ce Dokar Zaɓe ta 2022 ita ce matakin hana maguɗin zaɓe na huɗu.

Saura kwana 116 a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na 'yan majalisar wakilai da na majalisar dattawa.

Idan ba a manta ba, a farkon Oktoba shi ma Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, Farfesa Mahmood Yakubu, ya tabbatar da cewa maguɗi ba zai yiwu a zaɓen 2023 ba.

A labarin, ya ce INEC ta fito da hanyoyin kashe maguɗin zaɓe.

Yayin da hukumar ke ci gaba da tsare-tsaren gudanar da zaɓubbukan 2023, shugaban ya bugi ƙirji da cewa INEC ta samu nasarar toshe duk wata ƙofar da za a iya bi a yi maguɗi.

Da ya ke jawabi a wani taron da aka shirya a Cocin St. James na Ɗariƙar Angalika da ke Asokoro, Abuja, a kwanan baya, Yakubu ya ce INEC ta samu wannan gagarumar nasara ne ta hanyar ƙirƙiro tsarin tantance mai rajistar zaɓe na ƙeƙe-da-ƙeƙe, wato BVAS.

Yakubu, wanda Mataimakin Kakakin Yaɗa Labarai da Wayar da Kai ba hukumar, Chukwuemeka Ugboaja, ya wakilta, ya tsarin tantance mai karin rajistar hikima ce da basirar injiniyoin INEC ta kai su ga kirƙiro shi.

Ya ce BVAS zai ƙara wa INEC ƙarfin gwiwar tabbatar da cewa ta shirya zaɓe sahihi, wanda babu yadda za a iya yin maguɗi a lokacin zaɓe.

Ya ce: "Abu na biyu da zai ƙara wa zaɓen 2023 inganci shi ne sabuwar Dokar Zaɓe ta 2022. Sashe na 9 (6) ya bai wa INEC ikon daina yi wa mutane rajista kwanaki 90 kafin zaɓe. Daga nan ne kuma sai hukumar ta tankaɗe tare da tace rajistar ɗungurugum.

"Kuma mutane su fahimci cewa INEC ba ta iya soke rajistar kowa. Amma ta na da ikon soke rajistar wanda ya yi rajista sau biyu.

"Hanya ta uku da za a kawo ƙarshen maguɗin zaɓe ita ce aikawa da sakamakon zaɓe kai-tsaye ta na'urorin kafafen sadarwa na zamani daga rumfar zaɓe.

"Sannan kuma Sashe na 51 na Dokar Zaɓe ta 2021 ya nuna ƙin amincewa da sakamakon zaɓen inda adadin ƙuri'un da aka jefa a akwati su ka haura adadin yawan waɗanda aka tantance ta tsarin BVAS.

"Sannan kuma a zaɓen 2023, Sabuwar Dokar Zaɓe ta 2023 ta haramta wa INEC karɓar sakamakon da aka tilasta wa jami'in zaɓe bayyana sakamkon zaɓe."

Ya buga misali da zaɓen sanata na Jihar Imo a 2019, wanda duk da cewa tilasta jami'in INEC aka yi ya karanta sakamakon zaɓen, amma kotu ta amince da sakamakon. Ya ce a yanzu ƙarƙashin sabuwar dokar zaɓe, hakan ba zai yiwu ba.

Daga ƙarshe ya yi kira ga manya da masu ilimi mazauna birane cewa su daure su riƙa fita su na jefa ƙuri'a a ranar zaɓe.

Ya nuna damuwa kan cewa mazauna birane, musamman masu hali da manyan 'yan boko, ba su zuwa su na jefa ƙuri'a, duk kuwa da cewa sun san muhimmancin yin zaɓen.

No comments

Powered by Blogger.