Header Ads

Agajin marasa galihu: Ma'aikatar Jinƙai ta fara tantance sunayen waɗanda hare-haren 'yan bindiga ya shafa a Jihar Katsina

Gwamnatin Tarayya ta fara tattara sunayen waɗanda hare-haren 'yan ta'adda ya shafa a wasu ƙananan hukumomi a Katsina.

Aikin tantance sunayen wanda ake gudanarwa a ƙarƙashin Ma'aikatar Ayyukan Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa wadda Hajiya Sadiya Farouk ce Minista, zai ɗauki sunayen ne daga ƙananan hukumomi 11 domin su shiga cikin tsarin masu cin gajiyar shirye-shiryen da ma'aikatar ke samar wa marasa galihu a faɗin ƙasar nan.

Jagorar tawagar da ma'aikatar ta tura Katsina domin wayar da kan jama'a dangane da shirin ce ta bayyana haka.

Nadia Muhammad ta ce,  ''waɗanda hare-haren 'yan bindiga ya shafa su na cikin wani halin da su ke matuƙar buƙatar samun tagomashin canjin rayuwa."

Daga cikin tsare-tsaren da za a saka sunayen waɗanda za a tantance ɗin har da shirin bayar da tallafin kuɗaɗe ga marasa galihu, shirin bayar da jarin tallafawa domin a yi ƙananan sana'o'i, shirin N-Power, shirin ciyar da ɗalibai da sauran su.

Da ta ke jawabi, Funke Olatunji wadda ta wakilci Shugabar Sashen Ayyukan Musamman a ma'aikatar, wato Nadia Muhammad, ta ce matsalar tsaro ta kawo cikas sosai wajen kasa kai kayan agaji da gudanar da ayyukan jinƙai a wasu yankunan karkarar da 'yan bindiga su ka addabi jama'a da dama.

"Dalilin haka ne wannan ma'aikata ta fito da shirin tantance sunayen domin su riƙa cin moriyar ayyukan wannan ma'aikata kai-tsaye," inji ta.

Daga nan ta gode wa Gwamnatin Jihar Katsina dangane da ƙoƙarin da ta ke kan yi wa waɗanda hare-haren 'yan bingida ya shafa.

Wasu da hare-haren 'yan bindiga ya shafa daga ƙananan hukumomin Jibia,  Batsari da Kurfi, sun shaida wa jami'an shirin cewa su na buƙatar muhalli.
Hoto: Hajiya Sadiya Farouk

No comments

Powered by Blogger.