Header Ads

Mutanen da suka cike fom na tallafin Naira dubu 30 da aka ce na Tinubu ne sun fuskanci matsala

 Rahotannin da muka samu sun bayyana yadda ake kwashe wa dubun-dubatan 'yan Nijeriya waɗanda suka cike fom ɗin cewa Ɗan Takaran Shugaban ƙasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu zai ba da tallafin Naira 30,000 kuɗaɗensu daga asusun bakinsu, musamman masu ajiyan kuɗi a bankin GT da Zenith.

Idan ba ku manta ba, wani bayani ta soshiyal midiya ɗauke da cewa Ɗan takaran Shugaban ƙasar zai ba da tallafin N30,000 ya yi ta yawo a intanet cikin makon da ya gabata. Sai daga baya ya tabbata na ƴan damfara ne suka shirya, da sunan jama'a su cike domin su san bayanan asusun bankin mutum su kwashe masa kuɗi.”

“A halin yanzu haka, rashin jituwa ya auku a tsakanin masu tu'ammali da waɗannan bankunan guda biyu na GT da ”Zenith” duba ga yadda ake ta yin masu zari ɗai-ɗai na makudan kuɗaɗen su da ke cikin asusun bankinsu kai tsaye ba shamaki.”

“Bugu da ƙari waɗanda lamarin ya shafa sun koka, daga bisani sun tabbatar da cewa, aƙalla miliyoyin kuɗi ne ƴan damfarar nan suka kwashe daga asusun waɗanda suka cike wannan fam musamman masu amfani da “GT” da “Zanith” 

Sun kuma ƙara fashin baƙi da cewa hatta waɗanda suka cike amma da wasu bankunan can daban ba na “GT” da “Zenith” ba, lallai su ma su shirya domin ba barinsu ƴan damfarar nan za su yi ba, tunda mutum ya saka bayanan bakinsa, sai abin da ya gani.”

Hotunan wasu da ke Bankin GT na Bachirawa, Kano suna kokawa kan yadda aka damfare su ta Akawunt din su.

No comments

Powered by Blogger.