Hauhawar farashin man fetur: Ba wanda ya kara farashin mai a Nijeriya - NNPC
In za a iya tunawa, a baya kungiyar masu gidajen mai masu zaman kansu reshen jihar Kano sun shaidawa BBC cewa gwamnatin Nijeriya ta kara farashin man fetur a hukumance da kashi 8.8 inda a yanzu haka ya ke 185 wasu wuraren kuma 220 a sassan jihar Legas.
To sai dai kuma a yau Talata 31 ga wannan wata na Janairu shugaban kamfanin na NNPC, Malam Mele Kyari, ya musanta ikirarin kungiyoyin a wurin wani taro na masu ruwa da tsaki a matsalar mai da ake fama da ita a Nijeriya.
Malam Mele Kyari dai ya nemi mahalarta taron da su bayyana waye ya kara farashin tare da kawo hujjojinsu na sayen mai a sabon farashin.
Nijeriya dai kasa ce da Allah ya albarkace ta da man fetur, to sai dai hakan bai hana 'yan kasar fuskantar karancinsa da kuma rashin tabbas wajen farashin ba.
A wajen taron dai an bayyana yanayin jigilar man da kuma rashin daidaito wajen farashin sa a matsayin wasu daga cikin matsalolin man a Nijeriya.
Post a Comment