INEC ta gayyaci 'yan takarar shugaban ƙasa zuwa taron sa hannun amincewa a gudanar da zaɓe cikin ruwan sanyi
Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, tare da Mataimakiyar Sakataren Harkokin Ƙasashen Ketare ta Amurka mai kula da Al'amuran Afrika, Molly Phee, da Jakadiyar Amurka a Nijeriya, Mary Beth Leonard, lokacin ziyarar su a hedikwatar INEC don tattauna batun zaɓen 2023
Shugaban Hukumar Zaɓe na Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce dukkan 'yan takarar shugaban ƙasa za su bayyana a ranar Laraba, domin su sa hannu kan yarjejeniyar amincewar yarda a gudanar da zaɓe lami lafiya, ba tare da tashin hankali ba.
Yakubu ya bayyana haka a lokacin ganawar sa da 'yan jarida, bayan ya kai ziyara Makarantar Sakandire ta Garki, Abuja, inda ake bayar da horo ga Masu Sa-ido Kan Jami'an Zaɓe (SPO).
Shugaban na INEC ya kuma kai irin wannan ziyarar a Cibiyar Taro ta Ƙasa-da-ƙasa (ICC), inda a ce a can ne jihohi za su riƙa aikawa da sakamakon zaɓe ana tattarawa. Daga ƙarshe kuma a can ne shugaban na INEC zai bayyana ɗan takarar da ya yi nasara, tare da sakamakon da kowane ɗan takara ya samu.
Yakubu ya ce haka kuma ICC zai kasance Cibiyar Yaɗa Labarai.
Haka kuma Yakubu ya ce INEC ba za ta fuskanci matsalar ƙarancin kuɗi ba, bisa dogaro da alƙawarin da Gwamnan CBN, Godwin Emefiele ya yi wa shugaban na INEC, a lokacin da ya ziyarce shi.
Ya ce yawancin ayyukan da INEC za ta biya ma'aikata duk tura masu a asusun ajiyar su za ta yi.
Da ya ke magana kan ƙalubalen tsaro, ya ce wannan aikin jami'an tsaron ƙasa ne, kuma sun yi alkawarin babu wani gagararren da za'a bari ya haifar wa zaɓen 2023 da cikas.
Ya ce Kwamitin Wanzar da Zaman Lafiya ba Ƙasa da ke ƙarƙashin Tsohon Shugaban Ƙasa, Abdulsalami Abubakar ne zai shirya taron rattaba hannun amincewar da 'yan takarar za su yi a ranar Laraba, 22 ga Fabrairu, 2023, a Cibiyar Taruka ta Ƙasa-da-ƙasa (ICC), a Abuja.
Ya ce INEC ta kammala shirye-shiryen gudanar da zaɓen 2023 a cikin kwanciyar hankali.
Post a Comment