Header Ads

Mecece cutar 'Marburg' wadda ta bulla a nahiyar Afirka?

Hoton kwayoyoyin halittar cutar ke nan da ake gani da madubin likita 

A dai ranar Litinin, 13 ga watan Janairu ne, kasar Equatorial Guinea ta sanar da bullar cutar Marburg a karon farko a kasar. 

A yanzu haka dai, cutar wadda ta fara bulla a lardin Kie Ntem da ke yankin yammacin kasar, ta yi sanadiyyar rasuwar mutane 9, mutum 16 na dauke da cutar tare kuma da samun rahotannin alamomin da ke nuna cewa mutum na dauke da cutar.

Tuni dai hukumar lafiya ta duniya wato WHO ta aika da samfarin jini zuwa cibiyar ta da ke kasar Senegal domin tabbatarwa, kuma sakamakon ya nuna cewa daya daga cikin samfarin jini takwas da aka tura cutar Marburg din ce. 

A dai cikin shekarun 2022 da 2021 kasar Ghana da Guinea sun tabbatar da bullar cutar a kasashensu, haka kuma rahotanni sun nuna bullar cutar a kasashen Angola, Kenya, DR Congo, Afirka ta Kudu da kuma kasar Uganda.

Alamomin wannan cuta ta Marburg sun hada da zazzabi mai zafi, ciwon kai mai tsanani, amai da kuma zubar jini. Cutar ta kan yadu zuwa ga dan Adam ta hanyar jemage kuma tana cikin dangin kwayoyin cutar da ke haifar da cutar Ebola. 

A tsakanin mutane, cutar na yaduwa ta hanyar cudanya da ruwan da ke fita daga jikin masu cutar, kamar guminsu (zufa), yawo (miyau), ko kuma bawali (fitsari) da sauransu.

Wannan cuta, wadda cuta ce da ke kisa domin kuwa yawan wadanda suka mutu a bullar cutar a baya sun kai kashi 24 zuwa 88 a cikin 100, kawo yanzu dai ba ta da rigakafi kuma ba a gano maganinta ba.

Sai dai, hukumar lafiya ta duniya ta ce yiwa mutum karin ruwa da magance daya daga cikin alamominta kan taimaka wajen ganin mai dauke da cutar ya rayu.

Bayan haka, hukumar ta tura kwararrun likitoci zuwa gabashin Equatorial Guinea domin dakile yaduwar cutar tare da shirin aikawa da kayan gwajin kwayoyin cutar ciki harda rigunan kariya 500 tare da likitocin da za su yi amfani da su.

No comments

Powered by Blogger.