Header Ads

Nan gaba 'yan Nijeriya za su ga amfanin sauya fasalin kudi - Emifiele

Gwamnan CBN

Bayan ganawarsa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis, gwamnan babban bankin Nijeriya, Godwin Emifiele, a yayin da ya ke ganawa da manema labaru ya bayyana cewa sai nan gaba 'yan Nijeriya za su ga alfanun sauyin kudin da gwamnati ke kokarin aiwatarwa. 

Gwamnan babban bankin ya bayyana cewa an shirya sauya fasalin kudin ne domin cimma manyan muradu uku na gwamnatin Buhari, muradun nan kuwa sune rage rashawa da hada-hadar kudi ta haramtacciyar hanya, rage matsaloli na tattalin arzuki da kuma kawar da matsalar tsaro.

Gwamnan, wanda ya tabbatar da cewa ya gana da shugabannin bankunan kasuwanci a Nijeriya kimanin 15 tare da ba su umarnin fitowa da tsofaffin takardun kudi na naira 200 kamar yadda shugaban kasa ya yi umarni, ya ce duk da a yanzu ana jin radadin tsarin, amma za a ga alfanunsa nan gaba.

A dai ranar Alhamis ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin fitowa tare da cigaba da amfani da tsofaffin takardun kudi na naira 200 har zuwa 10 ga watan Afrilun wannan shekara.

No comments

Powered by Blogger.