Isra'ila ta kai hare-hare a birnin Damaskus
A wasu hare-hare ta jirgin sama wadanda Isra'ila ta kai birnin Damaskus da ke Siriya a ranar Lahadi, 19 ga watan Fabrairu, akalla mutane 5 ruka rasu kuma 15 suka jikkata, cikin wadanda suka rasu harda soja daya.
An dai ji karar fashewar abubuwa da misalin karfe 12:30 na dare, kuma kafar watsa labaru ta Syria Arab News Agency (SANA) ta bayyana cewa, "Na'urar tsaron sararin samaniya ta tunkari wasu hare-hare na sama a Damaskus."
Kamar yadda wata majiyar sojoji ta shaida, SANA ta ruwaito cewa akalla mutane biyar cikinsu da wani soja suka rasu, "gidajen kwanan jama'a da dama" sun rugurguje.
Kakakin Ma'aikatar Kasashen Waje na Siriya, Faisal Mekdad, ya bayyana cewa wadannan hare-hare dole a dauke su a matsayin "laifi ga daukacin bil-adama" domin an yi su ne a yayin da bai wuce sati biyu da fuskantar girgizar kasa wadda ta yi sanadiyyar rasa rayukan mutane sama da 5,800 ba a kasar.
Shugaban wata kungiya da ke kasar Ingila ta kare hakkin bil-adama da sa ido a Syria, Rami Abdel Rahman, ya bayyana harin da mafi muni, "Hare-haren na ranar Lahadi sune hare-hare mafi muni na Isra'ila a birnin Siriya." Shi kuwa Nasser Kanani, kakakin Ma'aikatar Kasashen Waje na Iran ya zargi Isra'ila ne da "yunkurin kara sa abubuwa su ta'azzara da lunka wahalhalun kasar Siriya, lokaci kadan bayan ta fuskanci mummunar girgizar kasa." Sai ya nemi majalisar tsaro ta majalisar dinkin duniya da ta yi wani abu a kan wannan al'amari.
Isra'ila ba ta ce komai dangane da hare-haren ba wadanda ke zuwa wata daya bayan ta harba mizayel a filin jirgin sama na kasa-da-kasa da ke Damaskus, sanadiyyar hakan kuwa mutum hudu suka rasu ciki harda sojoji biyu.
Wasu majiyoyin leken asiri na yamma guda biyu sun bayyana cewa inda aka kai harin wata cibiyar shiga da fitar kayayyaki ne na rundunar kariya ga juyin-juya hali ta Iran.
Kasashen Rasha da Iran dai duk sun yi Allah wadai da hare-haren, suna mai bayyana cewa suna yin barazana ga zaman lafiyar yankin.
Post a Comment