Header Ads

Jam'iyyu sun tura wa INEC sunayen ejan-ejan 1,575,301 waɗanda za su sa masu ido a rumfunan zaɓe 176,588

Wasu 'yantakarar shugaban ƙasa 

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta bayyana cewa jam'iyyu 18 waɗanda su ka fito takarar zaɓen shugaban ƙasa, sun bada sunayen mutum 1,574,301 a matsayin wakilan sa-ido, wato ejan-ejan ɗin su a lokacin zaɓen shugaban ƙasa.

Waɗannan adadin ejan-ejan su ne za su wakilci kowace jam'iyyya domin lura da yadda zaɓe ke gudana har zuwa lokacin tattara sakamakon zaɓe na kowane akwati da kowace rumfa.

Cikin sanarwar da INEC ta fitar a ranar Litinin, ta ce daga cikin su akwai ejan-ejan masu lura da yadda ake tattara sakamakon zaɓe, wato 'collation agents' har 68,057 daga jam'iyyu daban-daban.

Daga cikin ejan-ejan 1,574,301, NNPP ta tura wakilan ta na sa-ido har 176,200 a rumfunan zaɓe daban-daban a ƙasar nan.

Jam'iyyar LP ta tura ejan-ejan 134,874, PDP 176,588, APC 176,223.

INEC ta ce sauran jam''iyyu 14 kuwa sun tura adadin ejan-ejan na jimlar 910,426.

A ɓangaren ejan-ejan da za su lura da cibiyoyin tattara sakamakon zaɓe kuwa su 68,057, INEC ta ce NNPP ce ta fi sauran jam''iyyu yawan ejan-ejan a wuraren, domin ta na da 9,604.

Yayin da jam'iyyyar LP ke da ejan 4,859, ita kuwa PDP za ta tura guda 9,539, yayin da APC ke da 9,581.

Sanarwar INEC ta ce sauran jam'iyyu 14 na da jimlar ejan-ejan 34,474 kenan.

A Babbar Cibiyar Tattara Sakamakon Zaɓe ta Ƙasa a Ɗakin Taro na Duniya kuwa, jam'iyyun duka za su tura wakilai 27 jimla. PDP, APC, LP kowace wakilai biyu, NNPP wakili ɗaya, sauran jam'iyyu 14 kuma yawan na su wakilan guda 20 ne.

No comments

Powered by Blogger.