Header Ads

Karancin man fetur: Kungiyar fararen hula ta NCSES ta yi barazanar gudanar da zanga-zanga a duk fadin Nijeriya

Ababen hawa kan layi a gidan mai

Kungiyar fararen hula da tabbatar da cigaban tattalin arzuki mai suna Network of Civil Societies for Economic Sustainability (NCSES) ta yi gargadi ga kamfanin man fetur din Nijeriya, NNPC, cewa za su iya fara zanga-zanga a duka fadin kasar nan saboda karancin man.

Kungiyar, a cikin wata wasika da ta rubuta zuwa ga babban shugaban kamfanin mai na Nijeriya, NNPCL, Mele Kyari, sun bayyana cewa akwai yiwuwar daukar babban mataki a cikin kwanaki masu zuwa in har ba a yi wani abu ba domin rage yawan layi a gidajen mai.

Kungiyar fararen hular ta bayyana matsayar ta ne a cikin wata wasika wadda mai shirya tattaunawar kungiyar, Comrade Mohammed Shuaibu, da mataimakinsa, Comrade Nwogwugwu Bright, suka sanyawa hannu.

A cikin dai wasikar, kungiyar ta bukaci kamfanin na NNPCL ya yi bayani ya fayyace yadda abubuwa ke tafiya dangane da karancin man fetur a kasa tare da samar da hanyoyi domin magance matsalar. 


Kungiyar, kamar yadda ta bayyana a cikin wasikar, tana bukatar kamfanin ya yi duba ga wasikar a matsayin wani yunkuri na samar da daidaito, gujewa labaran shaci-fadi, dawo da fata da kwarin gwiwa ga 'yan Nijeriya, musamman matasa domin irin wahalar da suke sha wajen neman man fetur din domin gudanar da al'amurran su na yau da kullum.

Kungiyar, wadda ta bayyana cewa suna sauraron amsar wasikarsu cikin awowi 48, sun bayyana cewa suna karbar kiraye-kirayen gudanar da zanga-zangar domin hauhawar farashin mai, karancinsa da sauran matsaloli dama da suka lissafo, inda suka bayyana cewa har yanzu suna kan tattaunawa ne kuma suna fata kafin su yanke ranar daukar mataki, za su samu amsar da suke bukata.

No comments

Powered by Blogger.