Menene taron kungiyar tarayyar Afrika na wannan karon zai mayar da hankali a kai a birnin Addis Ababa?
Shugabannin kasashen Afirka sun hadu a birnin kasar Habasha, Addis Ababa, domin gabatar da taron shekara-shekara na kungiyar hadin kan na Afirka (African Union), wannan taro kuwa na wannan karon zai fara ne da maganar inda aka kwana wajen yarjejeniyar cinikayya a tsakanin kasashen na Afirka sai kuma ya mayar da hankali sosai kan abubuwan da ke damun nahiyar wadanda suka hada da yakoki da matsalolin da suka shafi abinci.
Sakamakon karancin ruwa da aka fuskanta a bangaren kasar Somaliya da munanan rigingimu a yankin Sahel da yankin gabashin Jamhuriyar Damakaradiyyar Kongo, taron hadin kan na Afirka da za a yi cikin kwanaki biyu zai yi duba cikin wadannan al'amurra tare da tabbatar da yarjejeniyar cinikayya da aka cimmawa ta shekarar 2020.
Wannan yarjejeniyar cinikayya dai itace mafi girma a duniya in an yi duba da yawan mutanen da ta kunsa, ta kuma hada da kasashe 54 cikin 55 na Afirka, kasar Eritrea ce kawai ba ta cikinsa.
Babban abinda za a mayar da hankali kansa shine samar da tsagaita wuta a yankin Sahel da kuma gabashin Jamhuriyar Damakaradiyyar Kongo inda 'yan bindigar M23 suka kwace iko da yanki babba kuma suka haifar da rigimar diflomasiyya tsakanin Kinsasha da Rwanda wadda ake zargi na goyan bayan 'yan tawaye.
Sakataren majalisar dinkin duniya, Antonio Guterres, ya bayyana cewa "Afirka na bukatar daukar mataki domin samar da zaman lafiya" dan ganin an hana hauhawar rigingimu da tabbatar da 'yancin damakaradiyya a nahiyar.
"Ina cikin damuwa game da hauhawar rigingimu na 'yan bindiga a gabashin Jamhuriyar Damakaradiyyar Kongo da kungiyoyin 'yan ta'adda a Sahel da sauran wurare." Guterres ya bayyana a farkon taron.
Ko a yayin wani dan karamin taro a ranar Juma'a, shugabannin kasashen gabashin Afirka guda bakwai sun yi kira ga kungiyoyin masu dauke da makamai da su bar yankunan da suka mamaye a karshen wata mai zuwa.
"Ba za mu iya kyale mutanen Jamhuriyar Damakaradiyyar Kongo ba, tarihi ba zai yi mana da kyau ba. Dole ne mu yi abinda ya kamata mu yi." Kamar yadda shugaban kasar Kenya, William Ruto, ya bayyana a wajen taron.
Post a Comment