An kora tawagar Isra'ila waje daga cikin taron kungiyar hadin kan Afirka
Jami'an tsaro sun nufi wurin da tawagar Isra'ila ta ke a cikin dakin taro na kungiyar hadin kan Afirka da ke Addis Ababa, Habasha, a safiyar yau Asabar tare da umartar su da su fice daga dakin taron kamar yadda kafar yada labarai ta Hebrew ta ruwaito.
A cikin wannan tawagar kuwa harda Sharon Bar-li, mataimakiyar darakta kan Afirka da ke Ma'aikatar Kasashen Wajen ta Isra'ila da sauran wasu mutane. Kamar yadda rahotanni ke nunawa, hakan ta faru ne a yayin bude taron kungiyar, inda jami'an tsaron suka nufi wurin da suke suka bukaci su bar dakin taron.
Wani babban jami'i da ke Ma'aikatar Kasashen Waje ta Isra'ila ya bayyana cewa sun fahimci cewa kasashen Aljeriya da Afirka ta Kudu ne ke bayan aiwatar da wannan al'amari, kamar yadda kafar watsa labarun Isra'ila mai suna Walla ta bayyana.
"Isra'ila na kallon wannan al'amari wanda aka fitar da mataimakiyar darakta a kan Afirka daga dakin taron hadin kan Afirka, duk kuwa da cewa tana da shaidar amincewa." Cewar kakakin Ma'aikatar Kasashen Wajen Isra'ila, Lior Hayat, kamar yadda kafar watsa labaru ta The Times of Israel ta ruwaito, "Abin bakin ciki ne ganin yadda kungiyar tarayyar Afirka ta kasance kasashe masu tsatstsauran ra'ayi na Aljeriya da Afirka ta Kudu suka yi garkuwa da ita, domin kiyyayya a karkashin ikon Iran."
"Muna kira ga kasashen Afirka da su nuna kin amincewar su da wannan al'amari wanda zai cutar da kungiyar hadin kan ta Afirka da nahiyar bakidaya." Ya bayyana
To amma da aka nemi jin ta bakin shugaban kasar Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, kan zarge-zargen na Isra'ila a kan Aljeriya da kasar ta Afirka ta Kudu a kan al'amarin sai kakakin shugaban kasar, Vincent Magwenya, ya ce, "Dole su kawo hujjojinsu."
Al'amarin kasancewar Isra'ila cikin kasashe masu sa ido a cikin kungiyar wani abu ne da ya haifar da rashin jituwa a tsakanin kasashen su 55.
A yayin gudanar da taron kungiyar na shekarar da ta gabata, an dakatar da muhawara a kan al'amarin domin gudun kada kuri'a wadda za ta haifar da barakar da ba a taba samu ba a cikin kungiyar hadakar ta Afirka.
Post a Comment