Canjin kudi: Gwamnatin jihar Kaduna ta umarci hukumomin jihar su karbi tsofaffin kudi
Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya umarci jami'an karbar haraji na ma'aikatu, hukumomi da cibiyoyin jihar su karbi tsofaffin kudade.
A cikin wani jawabi wanda mataimakin gwamnan na musamman a bangaren kafofin watsa labaru, Muyiwa Adekeye, ya karanto, ya bayyana cewa, "Domin kasancewa cikin biyayya ga umarnin kotun koli, gwamnatin jihar Kaduna na umartar ma'aikatu, hukumomi da cibiyoyin jihar da su tabbatar da cewa wadanda ke karbar masu kudade suna karbar kowacce naira, sabuwar da tsohuwar.
"Dokar jihar Kaduna ba ta yarda Ma'aikata su ruka karbar kudaden haraji da kansu ba.
"Jami'an da suke karbar suna da hanyar da suka samar domin karbar kudade kuma ana so su bi umarnin kotun."
Gwamna El-Rufai dai ya ki amincewa da umarnin shugaba Buhari na daina amfani da tsofaffin naira 500 da naira 1,000, kuma a yayin da yake jawabi kan canza fasalin kudin da kuma abubuwan da 'yan Nijeriya ke fuskanta a sakamakon hakan, ya zargi shugaban kasar da kyale wasu mugayen mutane su yi amfani da shi wajen haifar da rashin nasara ga jam'iyyar APC.
Gwamnan ya ma bayyana cewa wadanda suke amfani da Buhari domin kayar da jam'iyyar APC suna yi ne saboda dan takarar su ya fadi zaben fidda gwani da aka yi a cikin watan Yunin shekarar 2022.
Ya dai tabbatar da cewa tsofaffin kudaden suna nan a matsayin kudi da za a yi amfani da su a jihar Kaduna.
Post a Comment