Header Ads

Tinubu ya bukaci gwamnoni su yi watsi da umarnin Buhari, su tabbatar da ana amfani da tsofaffin kudi

Tinubu dan takarar shugaban kasa na APC

Dan takarar shugabancin Nijeriya a karkashin jam'iyyar APC, Ahmed Bola Tinubu, ya nemi gwamnonin Nijeriya da su yi watsi da umarnin Shugaban kasa Muhammadu Buhari na daina amfani da tsofaffin kudi na naira 500 da naira 1000. 

A cikin wata sanarwa wadda kakakin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC, Dele Alake, ya fitar a ranar Juma'a, dan takarar shugaban kasar na jam'iyyar APC ya nemi "duk gwamnonin da suke abokai" su bi sahun gwamna El-Rufai da sauran matakan gwamnoni na watsi da umarnin Buhari domin bin umarnin kotu.

Sanarwar ta kara da cewa kotu ce ke da fadar karshe, kamar yadda ake yi a sauran kasashe masu kundin tsarin mulki.

"Duka gwamnonin da suke abokai su yi gaggawar yin koyi da jawabin Kaduna nan take domin tabbatar da mutuncin kotu da kuma ikon doka a cikin kasa da sauran sassan duniya. Wannan shine amfanin kasancewar kasa wadda ke da tsarin mulki inda kotu ce ke da umarni na karshe kuma ake bin tsarin kasar Amurka." Kamar yadda takardar ta kunsa.

A ranar Alhamis 16 ga watan Fabrairu ne dai shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a cikin wani jawabi da ya gabatar ya bayyana cewa naira 500 da kuma naira 1000 ba za a cigaba da amfani da su ba, amma za a iya kaiwa babban bankin Nijeriya domin a canza su, a yayin da ita kuma naira 200 za a cigaba da amfani da ita har zuwa 10 ga watan Afrilu.

To sai dai wannan jawabi ya gamu da rashin amincewa a tsakanin gwamnoni, cikinsu kuwa har da gwamna El-Rufai, gwamna Abdullahi Ganduje da kakakin majalisar wakilai ta kasa, Femi Gbajabiamila, wadanda suka bayyana cewar kin bin umarnin na kotu a wannan hali gayyatar kasancewa ba gwamnati ne.

No comments

Powered by Blogger.