Header Ads

Zaben 2023: ‘Kun bar masu garkuwa da mutane su sace ni, kuma kuna son kuri'a ta?’

Aisha Mama da  ta bar kauyensu saboda gudun masu garkuwa da mutane

Mutane da yawa na rayuwa cikin tsoron yin garkuwa da su tare da rike su domin neman kudin fansa wanda kungiyoyin 'yan bindiga kan yi, musamman a arewa maso yammacin kasar nan, inda mutane da dama ya kasance dole su bar muhallansu. Wannan rashin tsaron na nufin cewa mutane da yawa a wannan yanki mai dauke da mutane masu yawa da suka yi rijistar zabe ba za su yi zaben ba na 25 ga watan Fabrairu. 

Wata muhimmiyar tambaya da ‘yan wannan yanki ke yi ita ce, ta yaya jam’iyyar da a gwamnatinta ake wannan ta’annatin za ta zaci samun kuri’un yankin, in dai zaben gaskiya da gaskiya za a yi?

"Kun kyale masu garkuwa da mutane sun dauke ni, yanzu kuma kuna son kuri'a ta?" Cewar Malama Maria Sani, da ke kauyen Bakiyyawa, wacce wata hanya kwara daya da ta tsaya kusa da wani icce ita ce kawai hanyar shiga kauyen da ke arewacin jihar Katsina.
Wannan wurin, wanda mafi yawan mutanen wurin manoma ne, ba wuri bane da mutum zai yi tunanin masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa da ke Nijeriya za su je.

Domin haka sai ya zama abin mamaki yayin da mutane dauke da bindigogi a kan mashina a cikin watan Satumbar da ta gabata suka fada wannan kauye tare da sace 'yan kauyen mutum 57.

Kamar saura, ita ma Maryam ta zabi shugaban kasa Muhammadu Buhari, amma wannan lokacin ba ta a ciki.

Shugaba Buhari zai sauka daga mulki bayan yin mulki a karo na biyu, a yayinda Bola Tinubu shi ne dan takarar jam'iyyar ta APC a wannan karon.

"Ya za a yi mutum na kallon duk wannan wahalar kuma ya zabi APC?" Lawal Suleiman ya bayyana, mamban jam'iyyar ne a da, amma yanzu kusan a iya cewa muryarsa ce kawai a kauyen mai yin kamfe ga Peter Obi na jam'iyyar Labour Party.

Da yawa daga cikin mutanen kauyan Bakiyyawa sun bayyana cewa za su goyi bayan jam'iyyar adawa ta PDP ne in har ma za su yi zabe.

"Idan har Buhari ya kasa yin maganin matsalolin kasar nan, to ba wanda zai iya." Kamar yadda Nana Samaila ta bayyanawa BBC, wata mata wadda ta gudu daga kauyenta a Batsari shekaru uku da suka gabata bayan hare-haren kungiyoyin 'yan bindiga.

Yarinyarta, Aisha Mama, ita ma ta gudu, ita da mijin ta daga kauyen Dangayya bayan hare-haren da ake kaiwa cikin dare sun sa ita da iyalanta sun yi makonni uku a cikin gonaki.

Malama Nana ta kasance mai fata sosai cewa shugaba Buhari, wanda tsohon shugaban kasa ne na mulkin soja, zai magance matsalolin kasar nan in an zabe sa a shekarar 2003, to amma a yanzu tana cike da mamakin irin tabarbarewar da abubuwan suka yi a karkashin mulkinsa.

An sace daruruwan yara 'yan makaranta an kuma sako su, gwamnan jihar ya taba cewa mutane su nemi makamai, wani abu da ke nuni da cewa ba abin da za a iya yi ga al'amarin. 

"Sun ruke matata har tsawon kwanaki 38," Abduljabbar Mohammed ya bayyana, wani ma'aikacin gwamnati da ake kallon yana da rufin asiri daidai gwargwado. Ya biya naira miliyan 1 (dalar Amurka 1,200, Euro 1,700) domin a sako ta.

"Na basu duka kudi na da kuma mashin dina, sannan na roke su kada su tafi da ni," Zaharadeen Musa ya bayyana, wani dan shekara 30, wanda mutane dauke da bindigogi wadanda aka fi sani da barayin daji suka kutsa inda yake da misalin karfe 1:00, tare da aiwatar da duk abin da suka yi niyya har na tsawon sa'o'i hudu ba tare da an dakatar da su ba, bayan sun kori wani ayarin 'yan sanda wadanda 'yan kauyen suka kira.

Ya taba biyan kudin fansa

Maria Sani, wata 'yar shekara 45, sun kama ta, amma ta samu ta gudu a yayin da 'yan bindigan suka nufi daji da mutanen da suka kama.

Bayan wannan al'amari, ta kasance cikin tunanin me zai faru da ita inda ba ta samu ta tsira ba, domin kuwa ba ta tunanin za ta iya biyan kudaden fansar.

Duk wadanda aka dauke sun samu kubuta amma bayan an kwashe watanni ana tattaunawa daga baya aka fanso su da kudi ko kuma da abubuwa masu daraja kamar mashina. Wadannan sace-sacen mutane da aka yi na nuni da yadda garkuwa da mutane ke kara ta'azzara ne tare da yaduwa- har ma wadanda ba su da komai ba su tsira ba.

Amma duk da haka, mutanen kauyen Bakiyawwa sai su dauki kansu masu sa'a in sun kwatanta da wani rahoto na ranar Juma'ar da ta gabata da ke nuna cewa 'yan bindiga sun kashe mutane sama da 100 a yanki a cikin Katsina.

Wadannan 'yan bindiga da ke yankin arewa maso yamma da kuma masu fafutikar ware kasar su babbar barazana ne ga zaben 25 ga watan Fabrairu, kamar yadda masu sharhi suka nuna.

Hare-hare a kan ofishoshin hukumar zabe ta INEC a shekarar 2019 ya sa an dage zabe da karin sati daya. Kona ofisoshin hukumar a yankin kudu maso gabas a kwanakin bayan nan na sa fargabar yiwuwar sake dage zaben a wannan karon, kodayake hukumomi sun ce ba za a yi wani jinkiri ba.

A cikin watan Disamba, hukumar ta INEC ta ce akwai matukar hatsari gudanar da zaben a wasu yankunan jihar Katsina, babu tabbacin me zai iya faruwa ranar zabe.

Wani farfesan shari'a, Chidi Odinkalu, yana hasashen yiwuwar zaben ya shiga cikin shari'o'i daban-daban, idan rashin tsaro ya hana zabe, wani dan takara kuma yana ganin an hana ya samu goyon baya.

A baya tsoron fadawa cikin rikici na sa mutane kauracewa zabuka a jihohin Imo, Anambara, Legas da Ribas, to yanzu kuma al'amarin masu garkuwa da mutane ya sa mutane da yawa ba su son shiga al'amurran zabe.

Manyan 'yan takara a zaben da ke tafe sun lura da cewa rashin tsaro wanda ke tare da hauhawar farashin kayan abinci, wanda hakan ya haifar da tsadar abubuwan rayuwa fiye da yadda aka saba gani shine babbar matsalar da ake fama da ita a yanzu.

Atiku Abubakar na PDP, Bola Tinubu na APC da Peter Obi na Labour Party, dukkaninsu suna yunkurin ganin sun samar da sauye-sauye ga yadda tsarin 'yan sanda ke tafiya, samar da cikakken taimako ga sojoji da kuma samar da walwala ga rayuwar al'umma da da sauransu.

To saidai abubuwan da suke shirin yi din ba wai ya bambanta da abubuwan shugaba Buhari, wanda aka zabe shi da alkawarin kawo karshen kungiyoyin da ke ikirarin ayyukan musulunci a arewa maso gabas, ya yi ba ne tare da samun nasara 'yar kadan. 

A yayin da ya iya rage irin ayyukan wadannan kungiyoyin a arewa maso gabas, rashin zaman lafiya ya karu a karkashin mulkinsa a yankin arewa maso gabas da kuma kudu maso gabas a karkashin mulkinsa.

"Ya rugurguza tattalin arziki, akwai rashin tsaro sosai." Mohammed Yusuf ya bayyana, wani manomi dan asalin jihar Katsina, wanda yanzu dole ya koma sayar da shayi da biredi a kan titunan babban birni da ke yankin, wato Kano.

Kano, Katsina da Kaduna wadanda akan kira da ke ‘K’ uku ana ganin su a matsayin wasu jihohi masu muhimmanci ga duk wanda yake fatan cin zabe a matsayin shugaban kasar Nijeriya. Jihohin na dauke da wadanda suka yi rijistar zabe masu yawa fiye da jihohin biyar na kudu maso gabas a Nijeriya.

Yawan kuru'un da Buhari ya samu a wadannan jihohin guda uku sun taimaka masa wajen cin zabe har sau biyu a jere, to sai dai a yayin da har yanzu wasu za su goyi bayan APC, ana ganin jam'iyyar ta rasa wannan muhimmin gurbin a wannan yanki mai fama da rashin tsaro.

Sati biyu da suka gabata hakan ya fito a fili a yayin da aka rinka jifar jirgin da ya ke ciki da ya je Kano.

Akwai ma dan takarar jam'iyyar NNPP, Rabiu Kwankwaso, magoya bayan sa kadai ke ganin shi zai ci zaben shugaban kasa, kuma yanzu ga wani muhimmi wanda zai iya takara rawa a wajen zabar wanda zai zama shugaban kasa mai zuwa.

Tsohon gwamnan Kano kuma tsohon ministan tsaro, Kwankwaso yana da magoya baya masu yawa a jihohin Kano da Jigawa.

Idan har ya kasance mai yawan kuri'u a Kano wadda ke da yawan wadanda suka yi rijista mutum miliyan shida, inda Legas ce kawai ta fi ta, to tabbas zai shafi sauran 'yan takara musamman wadanda ke a jam'iyyun PDP da APC.

Wannan zai iya taimakon jam'iyyar Labour Party wadda ba ta da karfi a yankin.

Kwankwaso kamar sauran 'yan siyasar Nijeriya, shi ma ya canza jam'iyya a lokuta da dama. A baya-bayan nan ya goyi bayan jam'iyyar PDP, kuma akwai jita-jitar cewa zai goya wa dan takarar jam'iyyar ta PDP, Atiku Abubakar baya, wanda shima daga arewacin Nijeriya ya fito.

"Shi da Obi ba za su ci ba, kodayake ya fi Atiku, wanda babban dan jari hujjah ne," Umar Yahaya, wani dalibi da ke karatu a jami'a mai tuka motar haya ya bayyana a Kaduna.

 "To amma duk wanda ya zabi APC to yana saka masu kenan a kan gazawar da suka yi." Ya ce a yayin da muka nufi tashar jirgin kasa ta Rigasa da aka bude ba da dadewa ba domin shiga jirgin kasa na Kaduna zuwa Abuja. Layin jirgin kasan ya kasance a kulle na tsawon watanni sakamakon wani mummunan hari wanda 'yan bindiga suka kai wanda ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutane da dama da kuma sace da dama.

A lokacin da Buhari ya bude jirgin kasan a cikin shekarar 2016, ya kasance wata alama ta cigaba a arewacin Nijeriya, to amma yanzu ya kasance alamar rikici da ke mamaye yankin.

No comments

Powered by Blogger.