Header Ads

Amurka ta sa sabbin takunkumi kan kamfanonin jiragen ruwan Iran

Ofishin da ke kula da siyasar kasashen wajen Amurka ya sa kamfanonin jiragen ruwa na kasar Iran biyu, kamfanin da ke kwashe kaya a tashar jirgin ruwa da kuma wani kamfanin da ke yin ayyuka a tashar jiragen ruwa a cikin jerin sabbin takunkuminta, a yayin da ta ke cigaba da ayyukan da ba su yi daidai da adalci ba ga kasar Iran. 

Washington ta yi ikirarin cewa kamfanonin da aka sawa takunkumin suna cikin "kungiyoyin da ke dauka, kaiwa da samar da sojoji da kayan aiki" da ke kara karfin dangantaka tsakanin Moscow da Tehran. Kamfanonin da aka sawa takunkumin sun hada da Khazar Sea Shipping Line da Nasim Bahr Kish wadanda kamfanonin jiragen ruwa ne na Iran biyu, sai kuma Grand Sea LLC, wani kamfani da ke yin aikace-aikace a tashar jirgin ruwa a Makhachkala da ke kasar Rasha.

Bayan haka, takunkumin ya hada da kamfanonin da suka shafi yarjejeniyar baya-bayan nan a tsakanin kasar Rasha da Iran na samar da titin jirgin kasa a yankin North-South Corridor.

Tehran ta suka da kakkausar murya kan shirin na Washington, inda ta bayyana cewa aikin jirgin kasan na Rasht-Astara yana a wani bangaren shirin da ya shafi makwaftaka ne wanda manufarsa ita ce hada kai domin tsaro, cigaba da samun daukaka baki daya.

A cikin 'yan kwanakin da suka gabata ne kasar Iran da Rasha suka sa hannu a wata yarjejeniya domin samar da titin jirgin kasan na Rasht-Astara, wanda wata hanya ce ta sufuri da ta hada titunan jirgin kasa da suke kasashen biyu a yanzu haka da kasar Azerbaijan.

Titin jigin kasan mai tsawon kilomita 162 zai hada birnin kasar Iran na Rasht da ke kusa da tekun Caspian da kuma Astara da ke kan iyaka da kasar Azerbaijan. 

Aikin, wanda manufar sa shine hada hanyoyin sufuri da na samun bayanai na kasashen Rasha, Azerbaijan, Iran da Indiya, ana gudanar da shi ne a karkashin tsarin International North-South Transport Corridor (INSTC). 

Tuni dai kakakin Ma'aikatar Harkokin Kasashen Wajen kasar Iran ya yi watsi da damuwar da gwamnatin Joe Biden ta nuna wadda "Ba ta da dalili mai karfi kuma wadda ba daidai ta ke ba" kan fadada hadakar safara da Iran ta yi da sauran kasashe, inda ya bayyana cewa yarjejeniyar baya-bayan nan a tsakanin kasar Rasha da Pakistan sakamakon bayar da muhimmanci da Iran ta yi ne a kan siyasar makwaftaka mai kyau.

No comments

Powered by Blogger.