An sako sauran 'yan matan makarantar Yauri da aka sace bayan kwashe kwanaki 707 a hannun wadanda suka sace su
Bayan kwashe kwanaki 707, an sako dalubai biyu da suka rage wadanda aka sace na Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Birnin Yauri, da safiyar ranar Alhamis, 25 ga watan Mayu, daga hannun wadanda suka sace su.
Kamar yadda PRNijeriya ta ruwaito, 'yan mata biyu da suka rage, Faida Sani Kaoje da Safiya Sani, an sako su ne bayan sasantawa mai tsawo tsakanin wani kwamiti na musamman wanda iyalan daluban da masu yi masu fatar alkhairi suka kafa da shugabannin 'yan bindigan.
Wani sanannen shugaban 'yan bindiga, Dogo Gide, ya kafe cewa sai gwamnatin jihar Kebbi ta cika wasu sharudda kafin a iya sako 'yan matan.
In dai ba a manta ba, a ranar 22 ga watan Afirilun shekarar 2023, kafar watsa labaru ta PRNigeria ta ruwaito sako wasu dalubai 'yan mata hudu wadanda ke da kananan yara biyu, bayan biyan kudin fansa masu yawa ga Dogo Gide.
Satuttuka bayan nan, a ranar 7 ga watan Mayu, wasu 'yan matan guda uku, Elizabeth Ogechi Nwafor, Esther Sunday da Aliya Abubakar, suma wadanda suka sace su din sun sako su.
An sako su din ne bayan hada kudaden fansa masu yawa daga iyaye da sauran masu ruwa da tsaki biyo bayan rashin gaggawa daga gwamnatin jihar Kebbi wajen biyan bukatun 'yan bindigan.
Dole sai da iyayen suka roki 'yan Nijeriya da su taimakesu da kudi domin su iya kubutar da 'ya 'yansu daga wadanda suka sace su din.
A cikin wata wasika wadda suka rubuta zuwa ga 'yan Nijeriya a cikin watan Janairun 2023, shugaba da kuma sakataren kungiyar iyayen yaran, Salim Kaoje da Daniel Alkali, sun bayyana cewa yaransu mata (masu shekaru tsakanin 12 da 16) na hannun wadanda suka sace su watanni 20 kenan.
"... Kuma wadanda suka sace su din suna neman a biya su naira miliyan 100 kafin su sako 'yan matan." Kamar yadda suka bayyana.
In dai za iya tunawa, dalubai 11 ne 'yan bindiga suka sace bayan sun afka makarantar ta su a ranar 17 ga watan Yuni na shekarar 2021.
Kuma a cikin watan Nuwambar da ya gabata, kafar watsa labarun ta PRNigeria ta ruwaito cewa wasu daga cikin 'yan matan sun zama iyaye, kuma kimanin hudu a cikinsu a yanzu haka na da juna biyu.
Kafar watsa labarun ba ta iya tabbatarwa ko kudin fansar da iyayen suka biya sun kai naira miliyan 100 kamar yadda 'yan bindigan suka bukata ba.
Post a Comment