Ba zan ba da kunya ba - Tinubu ya yi alkawari ga 'yan Nijeriya
Sabon Zababben shugaban kasar Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya sha alwashin ba zai ba 'yan Nijeriya kunya ba, ganin irin amana da girman abinda ake sa rai daga gareshi da kuma nauyin da aka dora masa yayin da ya ke karbar lambar girmamawa.
Zababben shugaban kasar ya bayyana haka ne a ranar Alhamis, 25 ga watan Mayu, yayin da ya ke jawabin amincewa bayan shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bashi lambar girmamawa ta kasa ta GCFR a fadar shugaban kasa.
Zababben shugaban kasar ya nuna cewa 'yan Nijeriya na da bukatar kasa wadda ta fi haka, inda ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta cigaba da tuntubar shugaban kasa Muhammadu Buhari in har bukatar hakan ta taso.
Tsohon gwamnan na jihar Legas ya zama shine mutum na 16 da aka ba lambar girmamawa ta kasa, GCFR, bayan Nnamdi Azikiwe, Obafemi Awolowo, Shehu Shagari, Olusegun Obasanjo, Abdulsalami Abubakar, Ibrahim Babangida, Earnest Shonekan, Sani Abacha, Umaru 'Yar Adua, Goodluck Jonathan da kuma Moshood Abiola.
Shugaban kasar ya ma mika lambar girmamawa ta GCON ga zababben mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima.
Post a Comment