Hukumar NDLEA ta kona haramtattun kwayoyi sama da kilo 23,000 da ta kwace a Enugu
Shugaban hukuma kuma shugaban sashen zartarwa na hukumar hana sha da tu'ammali da miyagun kwayoyi ta Nijeriya (NDLEA), Birgediya Janar Mohammed Marwa (mai ritaya) a ranar Laraba ya sha alwashin binciko duk wani lungu da sako a karkashin doka domin kakkabe miyagun kwayoyi daga kasar nan.
Marwa ya sha alwashin ne yayin da ake kona haramtattun kwayoyi masu nauyin kilo 23,721.7948 a bainar jama'a wadanda shiyyar hukumar ta NDLEA a Enugu ta kama a tsakanin shekarun 2018 zuwa 2021.
Shugaban, wanda daraktan aikace-aikace da bincike Samuel Gadzama ya wakilta, ya bayyana cewa nauyin "Cocaine" da aka kama shine kilo 21.699, "Heroin" kilo 14.828, "Amphetamine" kilo 0.0618, "Methamphetamine" kilo 24.347, "precursor chemicals" kilo 154.0, "Cannabis Sativa" kilo 23,225 da kuma "Pharmaceutical" kilo 281.759.
Yayin da ya ke kira ga 'yan Nijeriya da su hada karfi da gwamnati wajen yaki da ake yi kan shaye-shaye da safarar kwayoyi, Marwa ya bayyana cewa, "In har yadda ake fada da matsalar kwayoyi a yanzu ya cigaba tare da hadin gwiwa daga bangaren wadanda ba cikin gwamnati suke ba da kuma iyaye, zai kasance ba sauran wiwi ko kayayyakin da ke shafar kwakwalwa da za a kona a nan gaba."
A cikin jawabin shugaban, ya ma nuna godiyarsa kan taimako da rawar da kungiyoyin kasa-da-kasa irinsu the United States DEA, ofishin majalisar dinkin duniya kan kwayoyi da laifuffuka (UNODC), the UK board force, 'yan sandan kasar Jamus da kuma saura da yawa wajen nasarar da hukumar ta samu.
"Hukumar a 'yan kwanakin baya ta samar da layin kira wanda za a iya kira a kowanne lokaci a kwanaki bakwai na mako, 080010203040 ga duka 'yan kasa wadanda za su iya neman taimako a kan abinda ya shafi kwayoyi. Ga duk wanda ya ke a nan, ina cewa mu dage mu nuna dagaske muke yi wajen yaki da "abokin gaban mu baki daya" za mu iya." Ya bayyana.
Post a Comment