An samu kwanciyar hankali a Sudan yayin da yarjejeniyar tsagaita wuta ta haifar da sauki a yakin kasar
Wasu mutane zaune a bakin wani banki da aka kona a kudancin Khartoum a ranar 24 ga watan Mayu na shekarar 2023.
An ruwaito cewa an ji hare-haren jiragen sama a cikin dare a akalla yanki guda daya tun bayan tsagaita wutar da ta fara aiki a ranar Litinin, amma in banda haka mazauna yankuna sun bayyana cewa an samu kwanciyar hankali.
An dai amince da yarjejeniyar ne bayan wata tattaunawa da aka yi a Jeddah a ranar Asabar bayan shafe makonni biyar ana yaki ba karami ba a tsakanin sojoji da kuma dakarun kai dauki domin tallafawa ayyukan tsaro (RSF). Saudi Arabiya da Amurka ne ke kula da yarjejeniyar kuma niyyar ta itace a samu damar shigowa da kayan agaji.
Kasashen biyu a cikin wani jawabi na hadaka da suka fitar sun bayyana cewa ana ta shirye-shiryen kai kayan agaji cikin gaggawa.
Masu fafutika a kasar ta Sudan sun yi rubutu zuwa ga wakilin majalisar dinkin duniya a Sudan suna masu maraba da tsagaita wutar, sai dai sun bayyana cewa akwai cin zarafin hakkokin bil-adama da yawa ga fararen hula wanda suka bayyana cewa an yi yayin da ake yakin kuma ya kamata a yi bincike a cikinsa.
Kungiyoyin sa kai wadanda suke a gaba-gaba wajen samar da taimako a babban birnin kasar suna shirin karbar kayayyakin da aka kawo, duk da cewa mafi yawan kayayyakin agajin da aka kawo tashar jirgin ruwa ta Port Sudan da ke gabar tekun Red Sea har yanzu ba a rarraba su ba sakamakon hukumomi suna jiran tantancewar jami'an tsaro, masu fafutika da kuma masu aikin agaji.
Kungiyar agaji ta lafiya, MSF, wadda ke aiki a jihohi 10 na Sudan, sun bayyana cewa an samu rikici a bangarorin kasar ciki harda wasu biranen kasar da ke yammacin yankin Darfur.
Ma'aikatar lafiya ta Sudan ta bayyana cewa dakarun RSF sun kutsa tare da mamaye wani asibiti mai suna Ahmed Qassim hospital da ke Bahri kafin tsagaita wutar, suna kuma zaune a cikin wani asibiti da ke Bahri mai suna Alban Jadeed da safiyar ranar Talata. Dakarun na RSF sun zargi ma'aikatar da wallafa "karairayi."
Yarjejeniyar tsagaita wutar dai ta samar da fatar tsayar da yakin wanda ya sa mutane kusan miliyan 1.1 barin muhallansu, ciki kuwa har da sama da 250,000 da suka gudu zuwa kasashe makwafta.
"Fatar mu kwara daya itace yarjejeniyar ta yi nasara, saboda mu samu mu koma rayuwarmu kamar a da, mu ji cewa muna cikin amince, mu sake komawa aiki." Wani mazaunin Khartoum dan shekara 42, Atef Salah El-Din, ya bayyana.
Duk da cewa yakin ya cigaba duk da yarjejeniyoyi daban-daban, wannan ce ta farko da aka amince da ita a hukumance bayan sasantawa kuma wannan ce ta farko da ta hada da yadda ake bibiyar yadda ta ke.
Sakataren harkokin kasashen Amurka, Antony Blinken ya bayyana cewa bibiyar yarjejeniyar "zai kasance daban" ba tare da yin karin bayani ba.
Post a Comment