Ba za mu kwaso mata 160 da ke ikirarin su 'yan Nijeriya ne a Sudan ba tare da fasfo ba - Gwamnatin tarayya
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa mata 160 da ke ikirarin su 'yan Nijeriya ne ba tare da fasfo ba za su koma kasar.
Darakta Janar na hukumar agajin gaggawa ta Nijeriya (NEMA), Mustapha Ahmed, ya bayyana haka a Abuja a ranar Lahadi a yayin da ya ke jawabi ga manema labaru a kan cigaban da aka samu zuwa yanzu a kan kwaso 'yan Nijeriya daga kasar Sudan da ke fama da yaki.
Kamar yadda ya bayyana, duk da cewa matan sun yi ikirarin su 'yan Nijeriya ne, ba su da fasfo domin tabbatar da ikirarin nasu.
Shugaban hukumar ya bayyana cewa hukumar na bi a hankali domin gujewa kwaso wadanda ba 'yan Nijeriya ba.
In dai za a iya tunawa a yayin fara aikin kwaso 'yan Nijeriyan, hukumar 'yan Nijeriya da ke kasashen waje ta bayyana cewa akwai 'yan Nijeriya a kasar Sudan kimanin miliyan uku da kuma daluban ta 5,000.
Sai dai shugaban hukumar ta NEMA ya bayyana cewa bayan 'yan Nijeriya 2,518 da aka kwaso a jirage 15 kawo yanzu, ikirarin kasancewa 'yan kasar Nijeriya da wasu da yawa ke yi ba za a iya tabbatar da shi ba.
Ya bayyana cewa wasu daga cikin su sun yi ikirarin cewa kakannin-kakanninsu har zuwa hawa na biyar 'yan Nijeriya ne a yayin da su kuma an haife su ne a kasar Sudan, amma ba za a iya tabbatar da hakan ba.
Ya bayyana yadda wasu 'yan Sudan ke kokarin shiga motocin da aka kawo domin 'yan Nijeriya a Sudan din zuwa kan iyakar kasar Misra.
A yayin da aka tambayeshi ko nawa aka kashe domin kwaso 'yan Nijeriya daga kasar Sudan, Mustapha Ahmed bai fadi takaimaimai kudin ba, amma ya bayyana cewa Nijeriya ta biya dalar Amurka 22,662 a matsayin kudin fita a yayin da ta ke aikin kwashewar da kuma da kuma dalar Amurka 62,950 domin kudin bizar shiga kasar Misra.
Hukumar ta NEMA ta bayyana cewa kofofin damarmaki a bude suke ga duk wani dan Nijeriya mai tabbatattun takardu da ke da ra'ayin dawowa kasar.
A cikin 'yan Nijeriya 2,518 da aka dawo da su an bayyana cewa akwai wata mata mai ciki wadda ta haihuwa a yayin da ta ke jira a kwaso su. Yaron ta shine kawai karamin da a cikin wadanda aka kwaso din. Yaron dan kwana takwas a yanzu haka ana yi masa gwajin ciwon shawara a asibitin jami'ar Abuja da ke Gwagwalada.
Ba a rasa ran dan Nijeriya ba a yakin da ake yi a kasar Sudan. Sai dai an samu marasa lafiya mutum 23 a cikin wadanda aka kwaso din, a cikin su 10 sun samu kulawar likitoci a lokacin da suka iso inda 13 kuma aka kaisu asibitin 108 Nigerian Air Force Hospital da ke Abuja.
Post a Comment