Header Ads

Birtaniya na shirin samar da "daruruwan" jiragen yaki marasa matuka da makamai masu linzami ga Ukraine

Wani jirgin Birtaniya mara matuki

Kasar Birtaniya ta shirya samar da "daruruwan" jiragen yaki na kai farmaki marasa matuka ga kasar Ukraine wadda ke samun goyon bayan kasashen yamma, hakan kuma na zuwa ne daidai da lokacin da shugaban kasar ta Ukraine, Volodymyr Zelenskyy, ya kai ziyara Landan domin neman karin makamai.

"A yau Firaminista zai tabbatar da samar da makamai masu linzami na tsaron sararin samaniya da kuma jiragen yaki marasa matuka, ciki harda jiragen yaki marasa matuka masu cin dogon zangon da ya kai kilomita 200." Gwamnatin ta bayyana a ranar Litinin a yayin da kafofin watsa labarun cikin kasar suke yin rahoton cewa shugaban kasar ta Ukraine, Zelenskyy, na ganawa da Firaministan kasar ta Birtaniya, Rishi Sunak, a Chequers Court retreat.

"Duka wadannan za a samar da su ne a cikin watanni masu zuwa a yayin da Ukraine ke kara shiryawa domin kare kan ta" a cikin yakin da ta ke yi da sojojin kasar Rasha. Jawabin na Downing Street ya sha alwashi a yayin da Amurka ke kara tunzurawa a samar da manyan makamai domin sauraren abinda suka kira "spring counteroffensive" domin maido da wuraren da Rasha ta kwace daga Ukraine. 

"Wannan wani lokaci ne mai matukar muhimmanci ga kasar Ukraine wajen fafutikar ta kan mummunan yakin nuna fin karfi wanda ba ta zaba yi ba ko tonowa ba." Sunak ya yi ikirari kafin tattaunawar tasu a cikin gidan na musamman da ke kasar.

Masu sa ido a yadda al'amurra ke gudana a cikin kasar sun bayyana kalaman na Sunak a matsayin wadanda kishiyar hakikani suke nunawa in an yi duba da yadda Birtaniya ta shiga cikin yakokin da Amurka ta jagoranta a Afghanistan da Iraki a yayin tsaka da tarihinta na yin shisshiga ta hanyar soji da kuma yin mulkin mallaka a kasashe a fadin duniya.

Kasar Birtaniya dai ita ce kasar yamma ta farko da ta samarwa sojojin Kiev makamai masu linzami da ke cin dogon zango masu suna Storm Shadow.

Sai dai Moscow ta yi gargadin cewa za ta dora alhakin duk wani hari a kan kasar Rasha ga kasashen da ke samarwa Kiev makamai masu cin dogon zango, kuma tana da hakkin yin ramuwa.

Kasar Birtaniya, bayan Amurka, ita ce kasa ta biyu wajen samar da manya-manyan kayan yaki ga kasar Ukraine. 

Kafin dai yanzu Zelenskyy, wanda ya sha musanta amfani da makamai masu linzami masu cin dogon zango kan Rasha, ya fara tattaunawa da Firaministan Ingila wanda ya bayyana da "abokina Rishi."

Shugaban na Ukraine a cikin 'yan kwanakin nan ya ma tattauna da shugabannin kasashen Jamus, Italiya da Faransa inda ya ke nemansu da su kara samar da makamai kuma masu kyau ga Kiev domin yin fada da Rasha.

No comments

Powered by Blogger.