Header Ads

Hajjin 2023: Jihar Jigawa ta bayyana ranar da za ta fara kai alhazai 395 a tashin farko zuwa Saudiyya

Wasu maniyyatan Nijeriya

Hukumar kula da jin dadin alhazai ta jihar Jigawa ta bayyana cewa ta kammala duk wasu shirye-shirye domin kwasar maniyyata aikin hajji daga jihar zuwa Saudi Arabiya domin gudanar da aikin hajjin wannan shekarar.

Ana sa ran fara aikin kwasar alhazan ne daga ranar 27 ga watan Mayu ta hanyar kwasar alhazai 395.

Babban sakataren zartarwar hukumar, Alhaji Umar Labbo, ya bayyana haka ga kamfanin dillancin labarun Nijeriya (NAN) a Dutse a ranar Asabar.

Ana dai sa ran alhazai 1,622 ne za su yi hajjin na bana daga jihar ta Jigawa.

Labbo ya bayyana cewa ana sa ran za a fara da jigilar maniyyata 395 daga filin jirgin sama na kasa-da-kasa da ke Dutse wanda jirgin sama na Azman Air zai yi. 

Ya bayyana cewa tuni hukumar ta yi biza ga maniyyata 1,500 tare da basu kayan sawa iri daya (uniform) da sauran kayayyaki.

Sakataren ya bayyana cewa hukumar ta kai kudi kusan naira biliyan 4 ga hukumar kula da aikin hajji ta kasa (NAHCON) wanda ke nuni da kashi 100 na kudaden hajjin shekarar 2023 daga jihar.

Kamar yadda ya nuna, duk wasu shirye-shirye da masu ruwa-da-tsaki ciki har da jami'an tsaro duk an kammala su domin yin komai ba tare da matsala ba a jihar, inda ya kara da cewa gwamnatin jihar ta samar da muhalli mai kyau ga maniyyatan a Makkah.

Sakataren ya bayyana cewa duk wasu shirye-shirye da suka shafi tsaro da jin dadin alhazan an yi su a yayin da za su kasance a kasar mai tsarki.

No comments

Powered by Blogger.