Ina cikin mamakin cewa Blinken ya kira Tinubu a waya - Atiku
Dan takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, a ranar Laraba ya bayyana cewa yana cikin mamaki cewa sakataren harkokin kasashen wajen Amurka, Antony Blinken, ya kira zababben shugaban kasar Nijeriya, Bola Tinubu, a waya.
A cikin wayar da suka yi, Blinken ya bayyana aniyarsa ta cigaba da karfafa dangantaka a tsakanin Amurka da Nijeriya a gwamnati mai zuwa.
Sai dai Atiku, wanda ya yi takarar shugaban kasa a zaben da ya gudana a ranar 25 ga watan Fabrairun da ya gabata, ya bayyana amincewa da Tinubu da babban jami'in gwamnatin Amurka ya yi a matsayin abinda bai yi daidai da sakamakon da Amurka ta samu a kan zaben da ya gudana watanni uku da suka gabata ba.
"Ina cikin mamaki cewa @SecBlinken ya kira Tinubu, wannan bai yi daidai da matsayar Amurka a kan zaben shugaban kasa a Nijeriya na shekarar 2023 da ta bayyana a fili ba." Tsohon shugaban kasar ya rubuta.
"Wannan wani abu ne wanda hankali ba zai dauka ba, in an yi la'akari da cewa Amurka a matsayin ta mai kariya ga mulkin damakaradiyya, an bayyana mata da kyau duk yadda zaben na 25 ga watan Fabrairu ya ke.
"Bayar da amincewa a hukumance ga zaben da aka yi ittifakin an yi magudi a cikin sa a Nijeriya zai iya rage kwarin gwaiwar 'yan kasa da suka yarda da damakaradiyya da kuma karfin kuri'a @StateDept @POTUS @USinNigeria."
Ina cikin mamaki cewa @SecBlinken ya kira Tinubu, wannan bai yi daidai da matsayar Amurka a kan zaben shugaban kasa a Nijeriya na shekarar 2023 da ta bayyana a fili ba. Hankali ba zai dauki wannan ba in an yi la'akari da cewa Amurka a matsayinta na mai kariya ga damakaradiyya, an yi mata bayanai da kyau a kan zaben na 25 ga watan Fabrairu...
- Atiku Abubakar (@atiku) May 17, 2023
Post a Comment