Header Ads

Kasuwar masu sayar da mai a gefen titi ta karu, yayin da layukan gidajen mai ke ƙaruwar

Dogayen layuka a gidajen sayar da mai sun karu a birnin Abuja zuwa ranar Talata amma kuma akwai isasshen man ga masu sayar da shi a gefen titi a kan kudi naira 300 lita daya, kamar yadda kafar watsa labaru ta PM NEWS ta ruwaito.

Mafiyawancin gidajen man da ke birnin an kulle su yayin da kuma 'yan kadan da ke bude ana samun dogayen layuka.
Da yawa da ya kamata a ce sun kasance a wuraren ayyukansu dole su bi layi domin samun man ko kuma su saya a kan yadda ake sayarwa a gefen titi.

Layukan man dai sun dawo biranen Nijeriya ne bayan da shugaban kasa, Bola Tinubu, ya sanar cewa gwamnati za ta kawo karshen lokacin tallafin mai.

A dai ranar Litinin ne, bayan yin rantsuwar kama aiki yayin da ya ke jawabi, shugaban kasar ya bayyana cewa tallafin man fetur ba zai cigaba da kasancewa ba domin ba abu ne wanda zai iya dorewa ba.

Ya bayyana cewa kasafin kudin yanzu na shekarar 2023 ya kunshi tallafin man ne kawai zuwa watan Yuni, inda ya kara da cewa kudaden da za a yi tallafin da su za a mayar da su kan ayyuka, ilimi, kula da lafiya da samar da ayyuka.

"Muna jinjina ga gwamnatin da ta gabata na kawar da lokacin tallafin mai wanda ke kara amfanar da masu kudi fiye da talakawa. Tallafin ba zai cigaba da kasancewa ba sakamakon dalilin yin sa a yayin da ake cigaba da samun rashin kudade.

"A maimakon haka za mu mayar da kudaden a wuraren yin ayyukan gwamnati, ilimi, kula da lafiya da ayyukan yi wadanda za su bunkasa rayuwar miliyoyin mutane." Kamar yadda Tinubu ya bayyana.

Awowi bayan wannan sanarwa, dogayen layukan suka dawo biranen Nijeriya a yayin da ake tsaka da rashin tabbas kan me wannan tsarin zai haifar.

No comments

Powered by Blogger.