Kotun sauraron kararrakin zaɓen shugaban kasa ta ƙi amincewa da buƙatar nuna yadda zamanta ke gudana a talabijin kamar yadda Atiku da Obi suka nema
Kotun sauraron kararakin zaben shugaban kasa da ke Abuja ta ki amincewa da bukatar jam'iyyar Labour Party (LP), jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da kuma 'yan takarar shugaban kasarsu na nuna yadda zaman kotun ke gudana a gidajen talabijin.
Shugaban kotun, Justice Haruna Tsammani, ya ki amincewar ne a ranar Litinin, inda ya bayyana cewa bukatar ba ta da madogara.
Dan takarar shugaban kasa a karkashin PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya shigar da bukatar tasa ne a ranar 8 ga watan Mayu yana neman kotun da ta nuna yadda ake zaman kalubalantar nasarar da aka bayyana cewa Bola Tinubu na jam'iyyar All Progressive Congress ya yi a zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.
Jam'iyyar Labour Party da dan takarar shugaban kasar ta a zaben, Peter Obi, su ma sun nemi kotun sauraron kararakin da ta nuna yadda zaman ke kasancewa ta gidajen talabijin.
Wadanda suka shigar da karar da Farfesa Awa Kalu (SAN) ke wakilta sun nemi kotun da ta amince da bukatar. Abubakar Mahmoud (SAN) wanda ke wakiltar hukumar zabe mai zaman kan ta ta kasa (INEC), Wole Olanipekun (SAN) wanda ke wakiltar "zababben shugaban kasa", Bola Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima da Adeniyi Akintola (SAN) wanda ke wakiltar jam'iyya mai mulki ta APC, duk sun shigar da rashin amincewarsu tare da neman kotun ta ki amincewa da bukatar ta jam'iyyun na LP, PDP da kuma 'yan takararsu saboda rashin madoga da kuma haifar da tsaiko ga kotun.
Post a Comment