Header Ads

Minista Sadiya ta miƙa ragamar Ma'aikatar Harkokin Jinƙai ga Babban Sakatare

Minista Sadiya Umar Farouq na miƙa ragamar Ma'aikatar ta ga Babban Sakatare Dakta Nasir Sani-Gwarzo


Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta miƙa ragamar gudanar da ayyukan ma'aikatar ga Babban Sakataren ma'aikatar, Dakta Nasir Sani Gwarzo, bayan ta kammala aikin ta cikin gagarumar nasara.

Hajiya Sadiya ta riƙe ma'aikatar ne a matsayin ministar ta ta farko har tsawon shekara uku da rabi inda ta yi wa al'umma aiki tuƙuru babu gajiyawa.

Hajiya Sadiya ta miƙa wasu takardu ƙunshe a cikin kundaye biyu da ke bayyana ayyukan da ta yi a ma'aikatar a ranar Juma'a a Abuja, a ƙarshen Taron Duniya kan Ayyukan Agaji na Nijeriya (wayo Nigerian International Humanitarian Summit) karo na farko wanda ma'aikatar ta ɗauki nauyin shiryawa.

A jawabin da ta yi a taron, ministar ta gode wa Babban Sakataren da daraktoci da ma'aikatan ma'aikatar da na ofishin ta saboda gagarumin goyon bayan da su ka ba ta a dukkan tsawon wa'adin riƙe muƙamin ta.

Hajiya Sadiya Umar Farouq ta kuma yi kira ga ma'aikatan da su tsaya tsayin daka kan ƙoƙarin da su ke yi na ganin an cimma nasara a muradin Shugaba Muhammadu Buhari na 'yanto ɗimbin marasa galihu daga ƙangin fatara da yunwa.

Ta ce: “Ga ni a yanzu ina miƙa waɗannan takardun masu ƙunshe da bayanan riƙon ragamar da na yi a matsayin Ministar farko ta Ma'aikatar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa a cikin shekaru uku da rabi da su ka gabata. Na gode maku ƙwarai da gaske saboda goyon bayan da ku ka ba ni, a yau kuma na ke miƙa ragamar ga Babban Sakatare, Dakta Nasir Sani- Gwarzo”.

Da ya ke mayar da martani, Babban Sakataren ya gode wa Ministar, sannan kuma ya yi mata fatan alheri a duk inda ta sa gaba a shekaru masu zuwa.

No comments

Powered by Blogger.