Header Ads

Nijar za ta kare ni, in wani na neman yi min wani abu a Nijeriya - Buhari

 Tsohon shugaban kasar Nijeriya, Muhammadu Buhari 

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa zai tafi makwafciyar kasa Jamhuriyar Nijer domin kasancewa cikin kwanciyar hankali idan an dame shi ko kuma akwai matsala bayan ya bar ofishinsa a ranar 29 ga watan Mayu na shekarar 2023.

Shugaban kasar wanda ya bayyana haka a ranar Talata yayin da ya ke kaddamar da cibiyar hukumar kwastom ta naira biliyan 19.6 a Abuja, ya ce, "Na shirya in yi nisa da Abuja iya yadda zan iya. Na fito daga wani yanke da ke nesa daga Abuja." 

Duk da cewa ya bayyana ya fi son ya tsaya a mahaifarsa Daura da ke jihar Katsina, wadda ke arewa-maso-yammacin Nijeriya, ya ce, "Idan wani na son yin wani abu da karfi, ina da dangantaka mai kyau da makwaftana. Mutanen Nijer za su kare ni."

Buhari ya bayyana cewa tafiyar da ya yi ta farko a hukumance bayan ya shiga ofis a matsayin shugaban kasar Nijeriya itace ziyarar da ya kai Jamhuriyar Nijer, Chadi da Kamaru domin kara dinke dangantaka da su, kamar yadda The Sun ta ruwaito.

Mejo Janar din mai ritaya, wanda ya shugabanci Nijeriya a mulkin soja a tsakanin shekarun 1983 da 1985 ya kuma dawo a shekarar 2015 a karkashin mulkin damakaradiyya, ya bayyana cewa Jamhuriyar Nijer ta fi kusa da mahaifarsa kan Abuja, babban birnin tarayyar Nijeriya.

"Na fadi wadannan abubuwan kadan a matsayin abinda na yi imani da shi a kashin kai na domin kwanaki shida kawai suka rage min." Kamar yadda ya bayyana.

"Shi ya sa da na zama shugaban kasa, ziyarar farko da na kai ita ce a Nijer, Kamaru da Chadi saboda makwaftaka ta kai na da kuma matakin kasa. Idan ba ka samu yardar makwafcinka ba, kana cikin matsala.

"Idan ba ka cikin matsala, 'ya 'yan ka da jikokinka za su kasance cikin matsala.

"Saboda haka abu ne mai kyau in wanzar da dangantaka da makwaftana." Kamar yadda ya bayyana.

No comments

Powered by Blogger.