Rundunar sojojin hadin gwiwa a yankin tafkin Chadi sun tarwatsa 'yan ta'adda tare da kwace makamansu masu hatsari
Shugaban rundunar sojojin na hadin gwiwa a yayin da ya ke duba wasu makamai da aka samu daga mayakan ISWAP a 'yan kwanakin baya.
Rundunar sojojin hadin gwaiwa (MNJTF) sun tarwatsa 'yan ta'adda tare da samun makamansu masu hatsari a yankin tafkin Chadi.
A cikin wani jawabi a ranar Lahadi daga kakakin rundunar ta MNJTF, Laftanar Janar Kamarudeen Adegoke, ya bayyana cewa nasarar ta baya-bayan nan an yi ta ne a karkashin aikin da suka sawa suna "Operation Harbin Kunama."
"Aikin da MNJTF ke yi a yanzu haka ya rage kaifin 'yan ta'addan Boko Haram/ISWAP na yin ayyukansu a yankin tafkin Chadi.
"Yanayin aikin na rundunar MNJTF da kuma dagewarsu na cigaba da haifar da sakamako mai kyau.
"Bayan wani hari da 'yan ta'addan Boko Haram/ISWAP suka kai a kan sojoji a yankin Arege, wanda an dakile harin, sai rundunar sojojin ta gudanar da aikin binciko su a ranar 11 ga watan Mayu a baki daya yankin.
"An samo abubuwa da dama, ciki har da "Dushka Gun, Dushka Turrell da kuma konanniyar bindigar da ake sawa kan mota a yayin da aka tarwatsa 'yan ta'addan yayin arangamar." Kamar yadda jawabin ya nuna.
Ya ma bayyana cewa an yi aikin tattabatar da ba 'yan ta'adda a baki daya yankin Ferondiya da ke yankin tafkin Chadi kuma an yi shi cikin nasara domin tabbatar da cewa babu 'yan ta'addan a maboyarsu.
Kamar yadda jawabin ya nuna, abubuwan da aka samu daga 'yan ta'addan sun hada da bindigogi biyu da ake dorawa a kan mota, bindigogi biyu na harbo jirgin sama, wani bututu na bindigar RPG, bindigogin AK 47 guda biyu, bom din RPG guda daya da kuma tayoyin motar Toyota Buffalo Gun guda uku.
Sauran abubuwan sun hada da harsasai 387 rounds of 12.7 mm, 440 rounds of 7.62mm × 54mm da kuma 364 rounds of 7.62 mm × 50mm.
A yayin da ya ke jawabi a kan nasarorin da aka samu, kwamandan rundunar ta MNJTF, Mejo Janar G.U Chibuisi, ya yabawa sojojin kan aikin da suke yi tukuru, inda ya nemi da su cigaba da hakan.
Chibuisi ya ma yaba da kokarin bangaren sojojin da suka yi aiki ta sama wajen samun nasarorin da aka yi, inda ya nemi da a cigaba da hada hannu domin samun sakamako babba.
Post a Comment