Wasu 'yan bindiga sun kashe ma'aikatan ofishin jakadancin Amurka biyu da 'yan sanda biyu tare da kona su a Anambra
Wasu 'yan bindiga sun kashe 'yan sanda biyu da ma'aikatan ofishin jakadancin Amurka tare da sawa gawarwakinsu wuta a Amiye/Eke Ochuce da ke karamar hukumar Ogbaru a jihar Anambra.
Ma'aikatan ofishin jakadancin Amurka din an bayyana cewa sun zo ayyukan jin kai ne a yankin, sai 'yan bindigan suka tare su tare da harbe mutum hudu.
An bayyana cewa wasu sun samu raunuka yayin da suke gudu daga wurin da mummunan al'amarin ya afku. Al'amarin dai ya faru ne kusan karfe 3:30 na yamma a ranar Talata.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Anambra, DSP Tochukwu Ikenga, ya bayyana cewa hadakar jami'an tsaro sun tafi yin aikin ceto da binciko abubuwa a karamar hukumar ta Ogbaru bayan harin da aka kai a ranar ta 15 ga watan Mayu na shekarar 2023 da kusan karfe 3:30 na yamma kan jami'an ofishin jakadancin Amurka a kan titin Atani, Osamale.
Ikenga ya bayyana cewa batagarin sun kashe 'yan sanda biyu, ma'aikatan ofishin jakadancin Amurka biyu, inda kuma suka sawa gawarwakinsu wuta tare da motocinsu.
Ya kara da cewa bayan maharan sun ga tawagar hadakar jami'an tsaron sai suka dauke 'yan sanda biyu, direban motar ta biyu sai suka gudu, babu wani dan kasar Amurka a cikin tawagar.
Post a Comment