Wata dalibar makarantar Chibok da a yanzu ke da yara uku ta gudo daga 'yan ta'addan Boko Haram
Sojojin Nijeriya sun ceto wata dalubar makarantar Chibok, Saratu Dauda, bayan ta gudo daga 'yan ta'addan Ukuba a cikin dajin Sambisa da ke jihar Borno.
An dai bayyana cewa Saratu, wadda aka ceto a ranar 6 ga watan Mayu mai shekaru 25, ta auri wani mutum ne mai suna Abu Yusuf wanda kwararre ne a kan abubuwan da ke fashewa na kungiyar Boko Haram.
Kwamandan "Operation Hadin Kai," Mejo Janar Ibrahim Ali ne ya bayyana haka a ranar Litinin yayin da ya ke mika dalubar hannun kwamishiniyar harkokin mata da cigaban al'umma ta jihar Borno, Hajiya Zuwaira Gambo, a Maiduguri.
Ya bayyana cewa dalubar da aka sace tana da yara uku tare da mijin da aka tilasta mata ta aura, amma ta baro su tare da neman hanyar da za ta gudu daga cikin dajin, inda ya bayyana cewa ana kokari domin ganin an ceto yaran na Saratu Dauda daga mijin na ta.
Janar Ali ya bayyana cewa an kai ta asibitin sojoji na Maimalari domin kula da lafiyarta kafin a mika ta hannun gwamnatin jihar.
"Muna godiya ga Allah da aka ceto Saratu Dauda. Wannan zai taimake ki wajen samun rayuwa mai kyau tare da iyayenki da sauran 'yan uwanki da ke al'ummar Chibok.
"'Yan matan makarantar Chibok 76 yanzu suka gudo, a yayin da 107 'yan Boko Haram ne suka sake su a cikin shekarar 2018 daga cikin 276 da aka sace a ranar 14 ga watan Afirilun shekarar 2014.
"Dalubai 186 sojoji ne suka ceto su a yayin da 93 har yanzu suna hannun 'yan ta'adda.
"A tsakanin shekarun 2091 zuwa 2023, rundunar sojojin ta ceto 'yan matan makarantar Chibok 19, ciki har da 11 a cikin shekarar da ta gabata."
A yayin da ta ke na ta jawabin, kwamishiniyar harkokin mata da cigaban al'umma ta jihar Borno, Hajiya Zuwaira Gambo, ta bayyanawa manema labaru cewa gwamnatin jiha za ta dauki nauyin karatun Saratu Dauda ta yi karatun ta na sakandire da kuma na jami'a a jihar.
"Za a kaita "rehabilitation center" da ke Maiduguri domin haduwa da saura da ke koyon yadda za su dogara da kansu kuma su kasance masu amfani ga al'umma." Kamar yadda kwamishiniyar ta bayyana.
Post a Comment