Header Ads

Erdogan ya yi rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban Turkiyya a karo na uku

Shugaba Erdogan

Shugaban kasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya yi rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban kasa a karo na uku bayan aikin da ya yi a matsayin Firaminista har sau uku.

Erdogan, wanda ke da shekaru 69, ya yi nasarar samun wani wa'adin shekaru biyar ne masu zuwa domin ya jagoranci kasar a yayin zaben da aka sake maimaitawa a karo na biyu a satin da ya gabata.

Erdogan ya yi rantsuwar kama aikin ne a ginin majalisar kasar da ke Ankara a ranar Asabar, wanda hakan ya kara wa'adinsa zuwa karo na uku.

Za a bayyana sabuwar majalisar sa ne daga baya a ranar ta Asabar.

Manyan jami'ai daga kasashe 78 ne aka gayyata domin halartar bikin rantsarwar.

Wasu daga cikin baki a wurin bikin sun daga da mataimakin shugaban kasa na farko a Iran, Mohammad Mokhber, Firaministan Pakistan, Shehbaz Sharif, Firaministan Armenia, Nikol Pashinyan, shugaban kasar Azerbaijan, Ilham Aliyev da shugaban kasar Venezuela, Nicolas Maduro.

Shugaban kasar zai ma ci abincin dare tare da bakin a fadar Cankaya, tsohon gidan shugabannin kasashen Turkiyya, bayan bikin. Ana sa ran ya bayyana majalisar sa bayan cin abincin daren.

Erdogan dai ya yi nasara ne a zaben shugaban kasar wanda aka sake maimaitawa bayan ya samu kashi 52.18 cikin 100 na kuri'un da aka kada, fiye da kuri'un babban abokin takararsa Kemal Kilicdaroglu, wanda ya samu kashi 47.82 cikin 100 na kuri'un da aka kada, kamar yadda sakamakon da aka wallafa a hukumance daga hukumar zabe ta Turkiyya ya nuna.

"Bisa la'akari da sakamakon da aka samu, mun samu cewa an zabi Recep Tayyip Erdogan a matsayin shugaban kasa." Kamar yadda aka ruwaito shugaban majalisar koli ta zabe, Ahmet Yener, na fadi kamar yadda kafar watsa labaru ta kasar ta Anadolu ta bayyana a ranar Lahadi.

Yener ya bayyana a cikin wani jawabi kafin nan cewa zaben bai hadu da wani magudi ba ko cuwa-cuwa.

Erdogan ya yi nasara yayin jin ra'ayoyin mutane cikin kwanciyar hankali da kusan digo biyar fiye da abokin takararsa dan shekaru 74 a ranar 14 ga watan Mayu, sai dai ya kasa samun kashi 50 cikin 100 da ake bukata domin gujewa maimaita zabe.

Kilicdaroglu, wanda tsohon ma'aikaci ne kuma dan takarar jam'iyyun hadaka shida, shine ke shugabantar jam'iyyar Republican People's Party (CHP) wadda wanda ya kirkiro Turkiyya, Mustafa Kemal Ataturk, ya kirkiro.

No comments

Powered by Blogger.