Kai hari kan ayarin Yahaya Bello shiri ne domin a bata sunan Ajaka - Natasha Akpoti
'Yar takarar sanata a yankin tsakiyar jihar Kogi karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta bayyana cewa harin bayan nan kan ayarin gwamna Yahaya Bello shiri ne domin bata sunan Murtala Yakubu-Ajaka.
"Shiri ne kawai kan dan takarar gwamna a karkashin jam'iyyar Social Democratic Party (SDP), Murtala Yakubu-Ajaka." Natasha ta yi ikirari a cikin wani jawabi da ta fitar a ranar Lahadi a Lokoja.
Ta ma nemi hukumomin da suka dace da su gudanar da bincike a kan harin.
Ta bayyana cewa da Bello da Ajaka duka suna zargin junansu da yunkurin kisan kai, inda ta yi kira da a gudanar da bincike kafin a kasa shawo kan al'amurra.
"Harin shiri ne domin a bata sunan Ajaka, hukumar INEC ta ce bai cancanta ba a zaben gwamna na ranar 11 ga watan Nuwamba da ke tafe." Kamar yadda ta yi ikirari.
Sai dai kwamishinan watsa labarun jihar Kogi, Mista Kingsley Fanwo, ya bayyana cewa ya kamata ne Natasha ta yi bayanin ta ga jami'an tsaro ba ga kafofin watsa labaru ba.
"In tana nan lokacin da al'amarin ya faru, ya fi kamata ne ta je ta samu jami'an tsaro ta bayar da cikakken bayanin abinda ya faru.
"Amma in ba ta nan, ba ta yi adalci ga Bello ko Ajaka ba sakamakon wannan zargin." Kamar yadda Fanwo ya bayyana.
Post a Comment