Ƙasar Indiya ta gano dalili da mutanen da ke da alhakin haifar da hatsarin jirgin ƙasa mafi muni cikin shekaru masu yawa a ƙasar
Ma'aikatan ceto sun taru kusa da taragon jiragen kasan da suka lalace wajen neman wadanda suka tsira a wurin da jiragen kasan guda uku suka ci karo da juna a ranar 3 ga watan Yunin shekarar 2023.
Ministan hanyoyin jiragen kasa na Indiya, Ashwini Vaishnaw, a ranar Lahadi ya bayyana cewa an gano dalili da kuma mutanen da ke da alhaki wajen haifar da mafi munin hatsarin jirgin kasa da ya faru a kasar a cikin shekaru, inda ya nuna wata na'ura mai amfani da wutar lantarki ba tare da karin bayani ba.
"Mun gano dalilin hatsarin da kuma mutanen da ke da alhakin faruwarsa." Kamar yadda ministan ya bayyanawa kafar watsa labaru ta ANI, sai dai ya ce "bai dace ba" a bayar da cikakken bayani kafin rahoton bincike na karshe.
Yawan wadanda suka rasa rayukansu dai sakamakon hatsarin jirgin kasan da ya faru a ranar Juma'a kusa da Balasore a gabashin jihar Odisha, ana sa ran zai haura sama da 288.
"Canjin da ya faru yayin 'electronic interlocking," hatsarin ya faru ne a sakamakon haka." Wata kalma da ake amfani da ita da ke nufin tsarin da ake amfani da shi wajen hana jiragen kasa yin karo da juna ta hanyar shirya tafiyarsu a kan titunansu.
"Duk wanda ya yi hakan, da kuma ya abin ya faru, za a gano bayan cikakken bincike." Kamar yadda ya kara da cewa.
Akwai dai rudani dangane da yadda abubuwa suka faru, sai dai rahotanni sun bayyana jami'an titin jirgin na fadin cewa kuskuren sigina ne ya sa jirgin mai suna Coromandal Express da ke tafiya kudanci daga Kolkata zuwa Chennei komawa titin da ke gefe.
Ya afkawa wani jirgin kasa da ya kwaso kaya, sai kuma hatsarin ya yi sanadiyyar tunkude wani express wanda ya nufi arewaci daga cibiyar fasaha ta Indiya Bengaluru zuwa Kolkata da shi ma ya ke wucewa ta wurin.
Babban sakataren jihar Odisha, Pradeep Jena, ya tabbatar da cewa kimanin mutane 900 da suka jikkata aka kai asibiti.
Post a Comment